
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kula da Ci-gaban Sadarwa NITDA, ta fitar da saƙon ankara da al’umma game da sabon katin waya da ta gano (eSIM) da ake damfara da shi ta lambobin waya da rajistar data da kutse ga sanarwa gami da yaɗa saƙonnin bogi.
A halin yanzu katin ya shafin aƙalla na’urori guda biliyan biyu a faɗin duniya, lamarin da ke ƙara jefa tsaron harkar sadarwa cikin haɗari.
A wata sanarwa da ta fitar ga gidajen jarida ranar Juma’a, NITDA ta ce cigaba da yaɗuwar irinsa ka iya shafar biliyoyin salula da sauran nau’ukan na’urorin zamani a faɗin duniya.
A cewarta, hakan ya samo asali ne daga amfani da manhajar GSMA TS 48 Generic Test Profile (version 6.0 and earlier), wanda mafi yawancin manhajar rediyo ta compliance testing of eUICC (Embeddedd Universal Integrated Circuit Card) chips’ ya fi amfani da shi.
Akan haka ne hukumar ta kirayi al’umma da su yi taka tsan-tsan domin kauce wa shiga haɗarin da zai zama musu asara, yayin da hukumomin da ke da alhakin magance matsalar ke ƙoƙarin aiki a kai.
