Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da yadda ƴan ta’addan su ke ci gaba da kashe-kashen al’umma a jihohin Katsina, Filato, Neja da Benuwai da kuma wasu sassan Nijeriya.
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara kula da rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ƙarshen taronsu a Gusau yau Asabar.
Hakazalika a ranar 9 ga watan Agustan shekarar 2025 ne aka gudanar da zaɓen cike gurbi na ƙasa baki ɗaya, ƙungiyar ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin wuce gona da iri da ke tattare da rashin bin ƙa’ida, sayen ƙuri’u da tashe-tashen hankula daga gwamnatin APC a ƙasar.
Sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su ƙara sanya ido wajen kare ƙuri’unsu a nan gaba.
Ƙungiyar ta miƙa ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jihar Zamfara bisa rasuwar Sarkin Gusau, da ma da kuma al’ummar Jihar Oyo bisa asarar sarakunan gargajiya da aka yi a kwanakin baya.
Ƙungiyar ta Kuma jaddada cikakken ƙudurin su na taron kwamitin zartaswa na ƙasa karo na 101 na watan Yulin 2025, tana mai cewar zasu ƙara ƙaimi wajen tabbatar da babban taron jam’iyyar PDP na ƙasa daza ayi a ranar 15 ga watan Nuwamba ya samu gagarumar nasara.
Ta Kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar dasu kauce ma duk wani yunƙuri na daƙile taron da za a yi .
Ta bayyana jam’iyyar PDP a matsayin jam’iyya ɗaya tilo da za ta iya bin tafarkin dimokuraɗiyya, tare da dawo da Nijeriya bisa turbar shugabanci na gari da ci gaban ƙasa.
