Kwamitin faɗakar da al’umma mahimmanci mallakar katin zaɓe ya ziyarci shugaban hukumar zaɓe na Kano

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Kwamitin da gwamnatin Jihar Kano ta kafa Kan faɗakar da al’ummar Jihar Kano batun mahimmancin mallakar Katin zaɓe a jiya Juma’a ƙarƙashin Shugabancin kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin Gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fara ziyartar shugaban hukumar zaɓe na Jihar Kano Ambassada Zango A Abdu.

Da yake jawabi yayin ziyarar Shugaban kwamitin Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya yace dalilin wannan ziyara itace samun haɗin gwiwa wajen yadda aikin wannan kwamiti zai kasance matsayin su na hukumar zaɓe bai ɗaya ta Jihar Kano.

Kwamared Ibrahim Waiya ya kuma bayyana cewa mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya damu matuƙa na ganin wannan jiha ta cigaba da riƙe kambunta na matakin da take kai wajen tabbatar da riƙe ragamar matakin farko wajen yawan masu jefa ƙuri’a a faɗin ƙasar nan.

Haka kuma ya bayyana cewa akwai rawar da wannan hukuma za ta taka mai girman gaske wajen samun dukkan bayanai da wannan kwamitin ke buƙata dan gudanar da aikin su.

“Muna fatan wannan hukuma za ta bada dukkan goyon bayan da ake buƙata na daga ɓangaren samun ƙididdiga wajen mazaɓu da sauran abubuwan da ba’a rasa ba.”

“Gwamnatin Jihar Kano ƙarkashin jagoranci Gwamna Abba Kabir Yusuf a shirye take wajen bada dukkan goyon bayan da ake buƙata ga wannan Kwamiti.inji Kwamared Waiya.

Shima a nashi jawabin shugaban hukumar zaɓe na Jihar Kano Ambassada Zango A Abdu yace sunyi matukar godiya ga Allah bisa wannan ziyara ta neman haɗin kan wannan hukuma dan samun dukkan goyon bayan da ake buƙata.

Ambassa A Zango ya kuma tabbatar da cewa wannan hukuma a shirye take dan bada goyon bayan da ake buƙata a wannan aiki.

Ya zuwa yanzu muna da kimanin Katin zaɓe kimanin dama da 300,000 da ba karba ba a halin yanzu,wanda yakamata ace mutane sunzo sun karba dan tabbatar da samun rangwame wajen zaɓar ra’ayin da mutum ke buƙata.

Zango Abdu ya kuma buƙaci ƴan siyasa da su ƙara haɗa kan jama’ar su tun daga matakin akwatu har inda yakamata dan samun nasarar wannan aiki.

“Idan muka duba,zamu ga cewa Jihar Kano,jiha ce da tayi shura wajen batun kasuwaci da haɓɓakar tattalin arziki,dan haka mu ƙara ƙaimi wajen ƙara tabbatar da wannan kambu ta fuskar da muke kai a yanzu.”Zango A Abdu.

Haka zalika ya kuma bata tabbacin hukumar zabe ta Jihar Kano a shirye take wajen bada dukkan goyon bayan da ya kamata dan samun nasarar wannan aiki.

By ukarofi