Rundunar sojin sama ta tarwatsa maɓoyar Babaro tare da ceto mutane 76 Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta kai mummunan farmaki a maɓoyar fitaccen shugaban ɓarayin daji, Babaro, a tsaunin Pauwa da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara, inda ta ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara.

Babaro da tawagarsa na daga cikin waɗanda ake zargi da shirya kai mummunan harin baya-bayan nan a Unguwar Gidan Mantau, ƙaramar hukumar Malumfashi.

Harin da sojojin saman suka kai a Ƙanƙara,sun lalata sansanin da ya dade yana zama barazana ga al’ummomin yankin.

Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta tabbatar da cewa, cikin waɗanda aka ceto, har da dukkan mutanen da aka sace a harin Unguwar Mantau. Sai dai an bayyana cewa yaro ɗaya ya rasa ransa a lokacin musayar wuta.

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa wannan nasara ya nuna ƙarin kuzarin jami’an tsaro wajen lalata maɓoyar ‘yan bindiga, raunana ƙarfinsu, da kawo ƙarshen kisan gilla, satar mutane da tilasta biyan kuɗin fansa.

Ta kuma yaba da jarumtar rundunar sojin sama, rundunar sojin ƙasa, da sauran hukumomin tsaro kan ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a ƙauyuka da birane.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dr. Nasir Mu’azu Ɗanmusa ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa jami’an tsaro ta fuskar kayan aiki, bayanan sirri, da haɗin kan al’umma, har sai an kawar da barazanar ‘yan bindiga baki ɗaya.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu faɗakarwa da bayar da bayanan gaggawa da za su taimaka wajen tabbatar da nasarar ayyukan tsaro.

By ukarofi