Har yanzu Ɗangote ne wanda ya fi kowa kuɗi a Afirka – Forbes

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani karo, Alhaji Aliko Ɗangote ya sake kare matsayinsa na wanda ya fi kowane attajiri kuɗi a Afirka, inda ya zama ja-gaba a jaddawalin masu kuɗi na ‘Forbes Real-Time Billionaires’.

Lamarin da ya sa ya zama na 88 a sahun waɗanda suka fi kowa kuɗi a duniya bayan ya mallaki dukiyar da darajarta ta kai kimanin Dala biliyan 24.

A jaddawalin, wanda aka fitar a yau Asabar, ya nuna yadda Ɗangote ya yi fintinkau akan takwarorinsa na Nijeriya, kamar su Abdulsamad Rabi’u mai Dala biliyan 7.2 da Mike Adenuga mai Dala 6.3, sai kuma Femi Otedula mai Dala biliyan 1.5.

Hakan ya nuna cewa ya ninka Abdulsamad BUA sama da sau uku, Adenuga kusan sau huɗu sai sau sama da 16 ga na Otedula.

A shekarar 2008 ne Ɗangote ya fara shiga sahun masu kuɗi na Forbes, inda ya zama na ɗaya a jaddawalin tun a 2011 har zuwa yanzu.

Kamfaninsa da ke samar da siminti da suga gami da sabuwar matatar mai da ya gina sun taimaka masa wajen cimma nasarar samun gurbin a faɗin Nahiyar Afirka.

By Babaji