
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu ya yi watsi da batun da ke cewa Shugaba Bola Tinubu yana fama da rashin lafiya kuma an ba shi gado a wani asibitin Birtaniya.
Sanatan ya bayyana haka ne bayan sa’o’i 12 da ganawarsa da Shugaban Ƙasar inda ya ce lafiyarsa ƙalau kuma batun da ake yaɗawa ƙanzon kurege ne.
Tsohon gwamnan na Abia ya bayyana haka ne a gidansa da ke Maryland a Amurka ta wani faifan bidiyo da aka wallafa a Facebook, inda ya ce gajiya ce Shugaban ƙasar ya yi don haka hutu kaɗai ya ke buƙata.
Akan haka ya kirayi al’ummar Nijeriya da ƴan siyasa da su ƙaurace wa yaɗa kalaman cutarwa akan Tinubu, ganin cewa rashin lafiya abu ne da ka iya samun kowa.
Da yake magana akan tsare-tsaren tattali na Shugaban ƙasar, Kalu ya ce suna da tsauri ga al’umma, amma kuma akan hanya suke ta yadda za a amfana da su nan ba da jimawa ba.
A ƙarshe, ya yi kira da ƴan Nijeriya da su bai wa Tinubu dukkan goyon bayan da suka dace wajen ganin ya farfaɗo da martabar tattalin arziƙin ƙasar.
