Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A cikin ‘yan shekarun nan, matsalar ‘yan bindiga na cigaba da zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta, musamman a arewacin ƙasar nan. Harin da aka kai garin Malumfashi a Jihar Katsina na daga cikin fitattun abubuwan da suka tayar da hankalin al’umma, suke kuma ƙara sanya tsoro da firgici a zukatan jama’a. Babu shakka wannan harin ya janyo asarar rayuka, rushewar tattalin arziƙi da barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Idan za a iya tunawa a ranar Laraba ne gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar masallata 32 a dalilin mummunan harin, da wasu ’yan bindiga suka kai garin Mantau, na ƙaramar Hukumar Malumfashi da sanyin asubahin ranar Talata ta wannan mako mai ƙarewa, inda rahotanni suka tabbatar da cewa bayan kisan gillar ’yan bindigar sun kuma ci zarafin matan aure da ’yan mata a garin. Wannan al’amari ya tayar da hankalin jama’a da dama, da sanya ni kaina zubar da ƙwalla. Subhanallah!
Yawancin ’yan Nijeriya da dama musamman mazauna ƙauyukan Jihar Katsina da suka fi fuskantar waɗannan munanan hare-hare a yankin, da masu bibiyar al’amura a kafafen sada zumunta, suna kallon irin wannan harin a matsayin matsanancin rashin tsaro da ke daɗa kunno kai. Suna ganin harin na Malumfashi alama ce da ke nuna gazawar Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Katsina na rashin ɗaukar lamarin tsaron nan da muhimmancin da ya kamata a bashi ba, musamman a yankunan da ke fama da rikicin ‘yan bindiga, irin su ƙanƙara, Malumfashi, Funtua da sauran su.
A wani ɗan taƙaitaccen nazari da na gudanar na a zaurukan sada zumunta na fahimci yadda jama’a ke bayyana ɓacin ransu da damuwa kan lamarin, yayin da suke ɗora alhakin ƙara taɓarɓarewar lamarin tsaro kan Gwamnati da rashin nuna ƙwarewar jami’an tsaro a wasu lokutan. ‘Yan Nijeriya da dama na zargin gwamnati da rashin isasshen shiri da dabaru wajen daƙile ‘yan bindiga. Suna ganin akwai matsala wajen gudanar da aiki da tattara bayanan sirri da kuma rashin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.
Sun kuma ƙarfafa buƙatar shigar jama’a cikin ayyukan sa-kai da inganta tsaro a yankin, inda wasu ke ganin dole ne a ƙara mayar da hankali wajen ƙara ɗaukar matasa majiya ƙarfi don tallafawa jami’an tsaro, fahimtar matsalolitansu, musamman na tattalin arziƙi da zamantakewa, saboda irin wannan rashin jin daɗin ne ‘yan bindiga ke samun ƙarfi su ja ra’ayin wasu daga cikin matasan.
Wasu masu ra’ayin siyasa da zamantakewar al’umma na ganin cewa bai kamata kullum a mayar da martani da ƙarfi ba, amma a duba yiwuwar ɗaukar matakan sasanci ko tattaunawa da wasu daga cikin masu ƙoƙarin kawo tashin hankali, idan hakan zai iya kawo zaman lafiya na dindindin. Kamar yadda muka ga gwamnatin jihar ta sake farfaɗo da shi a kwanakin baya.
Jama’a da dama na takaicin yadda ake cigaba da rasa rayuka ba tare da an samu isasshen kamen masu aikata waɗannan laifuka ba, duk kuwa da kasancewar an san akasari daga cikin jagororinsu. Wasu su ma na ganin cewa ko da an kamo wasu ‘yan bindigan, ba a yi musu hukunci cikin gaggawa, wanda hakan ke ƙara wa masu laifi ƙwarin gwiwa.
Rahotanni sun rawaito wani ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Jibiya da Kaita a Majalisar Wakilai, Sada Soli yana kokawa game da harin ‘yan bindiga akan masallata a ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, inda ya yi zargin cewa baya ga jami’an tsaro sun san su, kuma yanzu ’yan bindigar ne ke riƙe da iko a wasu yankunan jihar.
Lallai ne Gwamnatin Tarayya ta karɓi ragamar tafiyar da harkokin tsaro a Jihar Katsina da Zamfara, ta ƙara yawan jami’an tsaro a yankin, a ƙara musu yawan makamai na zamani, kuma ta yi aiki da gwamnatin jihar da al’ummar yankin, don shawo kan matsalar cikin gaggawa. Babu tantama, wannan matsala ta samo asali ne daga haɗewar matsaloli da dama da suka haɗa da rashin ingantaccen tsaro, ƙarancin jami’an tsaro, rashin ayyukan yi musamman ga matasa, ƙarancin ilimi, da kuma rikici tsakanin makiyaya da manoma ko ƙabilanci tsakanin Fulani da Hausawa da yake daɗa samun gindin zama a yankin.
Lallai muna tunatar da gwamnati a dukkan matakai ta sani cewa, tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne ginshiƙin cigaban kowacce ƙasa, don haka ya zama wajibi gwamnati ta gabatar da dabarun haɗin gwiwa na musamman don shawo kan ƙalubalen ‘yan bindiga. Wannan ya haɗa da ƙarin horo da kayan aiki ga jami’an tsaro, ba da muhimmanci kan samar da bayanan sirri, da kuma ƙarfafawa hukumomin tsaro gwiwa.
Sannan gwamnati ta sani, matsalar tsaro bata da sauƙi, sai an haɗa kai da shugabannin al’umma, iyaye, matasa, da sauran masu ruwa da tsaki don samar da tsayayyen tsarin magance matsalar. Ilimantar da matasa da wayar da musu kai zai rage yawan shigar su cikin ƙungiyoyin ’yan bindiga da sauran ayyuka na karya doka.
Yana da muhimmanci Gwamnati ta ɗauki matakan samar da ayyukan yi ga matasa, bunƙasa ƙananan masana’antu, da samar da ababen more rayuwa zai taimaka rage yawaitar ‘yan bindiga da sauran munanan laifuka saboda rashin ayyukan yi. A ƙara yawan haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, gwamnatin jiha da ta tarayya, da kuma ƙasashen waje don samun damar daƙile shigo da makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma bayar da bayanai masu inganci. Sannan a tabbatar da ana gudanar da shari’a cikin gaggawa da adalci zai ƙara wa al’umma ƙwarin gwiwa da kuma hana masu aikata laifukan jin daɗin aikata laifi.
Na yi imanin cewa, samun nasarar magance matsalar ‘yan bindiga a Malumfashi da duk yankunan da abin ya shafa, ya rataya ne a kan gwamnati da al’ummar jihar, matuƙar sun haɗa kai yadda ya kamata. Sannan su samar da hanyoyi na amfani da dabaru iri-iri na inganta da cigaban zamantakewar al’umma, domin kaucewa ci gaba da taɓarɓarewar tsaro a jihar. Haka kuma, tilas a tallafa wa al’umma ta hanyar faɗakarwa da ƙarfafa musu gwiwa ta hanyar samar da ayyuka yi ga matasa, saboda yawancin ‘yan bindiga na gudanar da aikinsu ne saboda rashin hanyoyin samun ayyukan dogaro da kai.
Duk da wahalhalun da ake fuskanta, nagarta da hangen nesa zai taimaka wajen samun cigaba da ingantaccen tsaro mai ɗorewa a Nijeriya.
Muna roƙon Allah Ya ba mu zaman lafiya da tsaro a garuruwan mu, jihohin mu da ƙasa bakiɗaya. Amin
