Babaji

5698 Posts

An san masu ɗaukar nauyin ta’addanci amma ake kare su, inji tsohon kwamandan sojoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Manjo Janar Ɗanjuma Ali-Keffi (mai ritaya), wanda kwamanda ne na rundunar sojoji a shiyya ta ɗaya a Jihar Kaduna, ya yi ikirarin akwai mutane masu ƙarfin faɗa a ji da ke alaƙa da ɗaukar nauyin ayyukan ta'addanci da satar mai a Nijeriya, waɗanda binciken jami'an tsaro ya fallasa su amma kuma aka ƙyale su. A wata hira da tashar Arise ranar Alhamis, Janar Ali-Keffi, wanda ya taɓa jagorantar atisayen Service Wing (OSW), da ke da alhakin katse hanyoyin ɗaukar nauyin ta'addanci, ya ce akwai binciken da ya bayyana waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'addanci da…
Read More

Ba na gasar iko da kowane sarki, inji Alafin na Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Oba Akeem Owoade, wanda shi ne Alafin na Oyo ya bayyana cewa, shi ba mutum ne mai gasar iko ba da kowane sarki a ƙasar Yarbawa ko kuma a wani waje na daban. Sarkin ya faɗi haka ne a wata takarda da Daraktan yaɗa labaransa, Bode Durojaiye ya fitar kan rashin jituwa da ke tsakanin sa da Ooni na Masarautar Ife, wato Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi. Rikicin nasu ya samo asali ne a lokacin da Oonin ya bada sarautar Okanlomo ga wani ɗan kasuwa mai suna Dotun Sanusi yayin ƙaddamar da shafin gargajiya a…
Read More

Alƙalin ‘Viral TV’, Frank Caprio ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Frank Caprio, wanda daɗaɗɗen Alƙali ne na kotun birni ta 'Providence Municipal' a Amurka kuma shahararre a kafar talabijin, ya rasu bayan shafe shekaru 88 a duniya. Ɗansa, Frank T. Caprio ya sanar da hakan a ranar Laraba a wani rubutu ta Facebook a madadin iyalan marigayin. Ya ce, mahaifin nasu "ya rasu ne cikin aminci yana da shekaru 88 bayan fama da cutar daji ta ƙundu ta tsawon lokaci." Marigayin sananne ne akan tsayar da gaskiya da adalci a matsayinsa na alaƙali da ma wajen haka, lamarin da ya sa ya zama jigo…
Read More

Badaƙala: EFCC na neman sirikin Atiku, Bashir Haske ruwa a jallo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta ayyana sirikin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar kuma ɗan kasuwa, wato Abdullahi Bashir Haske a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zargin sa da hannun a badaƙalar wasu kuɗaɗe. Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya bayyana hakan a wata takarda da aka sanya a allon sanarwar ofishinsu, ranar Alhamis. A cewar EFCC, Haske mai shekaru 38 yana da hannu a kitsa makircin babban laifi da kuma sauya akalar wasu kuɗaɗe. Don haka hukumar ta wallafa hotonsa a takardar da sunan tana nemansa ruwa-a-jallo. Ta…
Read More

Tsaro: Ya kamata kowane ɗan Nijeriya ya koyi yadda ake kare kai, inji Babban Hafsan Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya kirayi al'ummar Nijeriya da su koyi yadda za su riƙa kare kansu daga farmakin miyagu saboda ko ta-kwana. Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels, Janar Musa ya ce horon kare kai abu ne mai muhimmanci ga ɗan Nijeriya kamar yadda koyon tuƙi ko ninƙaya acikin al'umma ke da muhimmanci a hali na yaƙi ko akasin haka. "A Turai, ninƙaya wajibi ne. Koyo da karantarwa akan tsaro ma wajibi ne, saboda sai ka san mene ne tsaro." Haka kuma, Babban Hafsan…
Read More

Majalisar Wakilai ta gayyaci kamfanonin DisCos 11 kan bashin tiriliyan N2.6

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin Asusun Ƙasa na Majalisar Wakilai ya gayyaci kamfanonin raba wutar lantarki (DisCos) guda 11 bisa bashin da asusun tarayya yake bin su. A ranar Laraba yayin zaman majalisar aka tattauna batun sakamakon bincike ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa Bamidele Salami bayan gano haramtattun ayyuka a fannin lantarkin Nijeriya a rahoton da Odita Janar ya fitar na 2021. Darakta Manaja na Kamfanin Kula da Kasuwancin Lantarki a Nijeriya (NBET), Johnson Akinnawo ya tabbatar da cewa an gabatar da takardun basusuka ne a gaban kwamitin domin ɗaukar matakan da suka dace a kai. A cewar rahoton…
Read More

Jakadan Nijeriya a Kamaru, Ambasada Coker ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ma'aikatar Harkokin Waje ta sanar da rasuwar Ambasada Taofik Obasanjo Coker, wanda shi ne Jakadan Nijeriya a Buea na Jamhuriyar Kamaru. A sanarwar da Kakakin ma'aikatar, Kimiebi Ebienfa ya fitar, Ambasada Coker ya rasu ne a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025 bayan fama da wani gajeren rashin lafiya. Marigayin ya kasance mai jajircewa akan harkokin difulomasiyya da sadaukarwa wajen yi wa ƙasa hidima, wanda ya wakilci Nijeriya bisa kishi da nuna ƙwarewarsa. Sanarwar ta ƙara da cewa, rashinsa zai haifar da babban giɓi ga ɗaukacin ƴan difulomasiyya da ma Nijeriya baki ɗaya. Gabannin…
Read More

Harin Masallaci a Katsina: ‘Yan bindiga sun karɓe iko da wasu yankunan jihar, inji ɗan majalisa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Jibiya/Kaita a Majalisar Wakilai, Sada Soli ya koka game da harin ƴan bindiga akan masallata a Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina. Iftila'in ya auku ne kwanaki uku da suka gabata a wani masallaci yayin sallar asuba, inda ya ce baya ga jami'an tsaro sun san su, kuma suna riƙe da iko a wasu yankunan jihar. A wata hira da shi ta gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, ɗan majalisar ya ce ƴan bindigar da suka kai harin, suna gudanar da harkokinsu cikin walwala a ƙauyukan da ke…
Read More

Ooni na Ife ya yi wa Alafin na Oyo martani kan umarnin soke bada sarautar Okanlomo ga Ilaji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ooni na Masarautar Ife, wato Oba Adeyeye Ogunwusi ya yi wa Alafin na Oyo, Oba Abimbola Owoade martani bisa kalamansa na umarnin ya soke sarautar Okanlomo na ƙasar yarbawa da ya bai wa ɗan kasuwa Dotun Sanusi da ake kira da Ilaji. A ranar 18 ga watan Agusta, 2025 Alafin na Oyon ya nemi Oonin da ya gaggauta soke bada muƙamin, inda gargaɗe da cewa ya yi hakan cikin kwana biyu ko kuma ya fuskanci hukunci. Da yake magana a ranar Talata, Oonin ya bayyana hakan a matsayin abinda ba shi da tasiri ga…
Read More

Tinubu ya soke harajin kaso 5 na Telekoms

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ana sa ran miliyoyin ƴan Nijeriya da ke amfani da kayayyakin telekom za su samu rahusa bayan da Shugaba Bola Tinubu ya soke shirin kaso biyar na harajin harkokin kamfanonin akan kwastomomi. Harajin, wanda aka gabatar a kundin dokar kuɗi ta 2020 ya sha fuskantar suka daga masu ruwa da tsaki. Da yake tabbatar da ci-gaban a ranar Talata a Abuja, Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), Dakta Aminu Maida ya sanar da cewa harajin, wanda da fari aka dakatar da shi, an cire shi baki ɗaya daga kundin dokar yanzu. An gabatar…
Read More