Tinubu ya soke harajin kaso 5 na Telekoms

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ana sa ran miliyoyin ƴan Nijeriya da ke amfani da kayayyakin telekom za su samu rahusa bayan da Shugaba Bola Tinubu ya soke shirin kaso biyar na harajin harkokin kamfanonin akan kwastomomi.

Harajin, wanda aka gabatar a kundin dokar kuɗi ta 2020 ya sha fuskantar suka daga masu ruwa da tsaki.

Da yake tabbatar da ci-gaban a ranar Talata a Abuja, Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), Dakta Aminu Maida ya sanar da cewa harajin, wanda da fari aka dakatar da shi, an cire shi baki ɗaya daga kundin dokar yanzu.

An gabatar da harajin ne a zamanin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da nufin ya taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga ga gwamnati, lamarin da ƙungiyoyin kwastomomi da masu-ruwa-da-tsaki na masana’antu suka riƙa kushewa.

Sun bayyana hakan a matsayin abinda ba iya ƙarin kuɗin kira ko data zai shafa ba, har ma da rayuwar yau da kullum duba da matsin tattali da al’umma ke fuskanta a ƙasar.

Tun a watan Yulin 2023 Shugaba Tinubu ya umarci a dakatar da harajin domin tasirinsa ga harkokin kasuwanci da ma al’ummar ƙasa.

By Babaji