Daga MD ASNANIC
1.0 Gabatarwa
Ilimin Ginin Jumla wanda masana suka laƙaba masa suna _Syntaɗ,_ ilimi ne da ya ƙunshi tsarin haɗa jumla da halayen da ke wakana a cikinta, tun daga tsarin yadda take ginuwa ta hanyar A+A+K (S+ɓ+O) —watau Aikau + Aikatau + Karɓau da kuma tsarin ɓangarorinta biyu: Yankin Suna da Yankin Aiki/Bayani. Haka zalika wannan fage na Ginin Jumla yana tattare da ƙunshiyar bayanai game da kafatanin rukunnan Nahawun Hausa.
Wannan rubutu ya yi nazari ne game da dacewar wasu jumloli da cikin ke littattafan wasu marubuta na Hausa a bisa tsarin Ginin Jumla ko kuma rashin dacewarsu.
2.0 Jumla da karikitan cikinta
Yahaya, (2007) da Zarruƙ, (2012) sun bayyana jumla a matsayin jerin kalmomi masu alaƙa a wajen tsari, waɗanda kuma suke bayyana wata manufa cikakkiya.
Kamar yadda matashiya ta gabata, jumlolin Hausa ana gina su ne bisa tsarin Aikau (Subject) + Aikatau (ɓerb) + Karɓau (Object), waɗannan su suke haifar da yankuna biyu da jumlar Hausa ke da su —Yankin Suna (YS) da Yankin Aiki/Bayani (YA/B). Abubuwan da ake samu a Yankin Suna sun haɗa da: sft¹ da K² da sft³. A Yankin Aiki/Bayani kuwa ana samun Zagin Aikatau (ZA) da Aikatau (A) da Yankin Suna Na Biyu (YS²) da kuma Bayanau (Byn). Domin sauƙaƙa fahimta za mu iya kallon yankunan jumla kamar haka:
YS = sft¹ + K² + Sft³
YA = ZA + A + YS² + Byn
A tsari irin na yankin jumla, Aikatau da Bayanau (abubuwan da nake nazari a kansu) ana tarar da su ne a Yankin Aiki/Bayani, wanda kuma wannan yanki shi ke zuwa a ƙarshen jumla.
3.0 Inda gizo ke saƙar
A yankin farko (Yankin Suna) na jumla ne ake ambaton wanda ya yi aiki (Aikau) yayin da a yanki na biyu (Yankin Aiki/Bayani) ake ambaton aikin da Aikau ya aikata, Zarruƙ (2012:69). Haka nan kuma dai, a wannan yanki na biyu ake samun Bayanau. Ke nan duk jumlar da aka fara ta da Aikatau ko Bayanau ba a sanya Aikatau ɗin da Bayanan a muhallinsu na asali ba, ya zama an maido da su Yankin Suna na jumla ke nan. Ga misalan wasu jumloli daga cikin littattafan Hausa:
3.1 Farawa da Aikatau/Suna ɗan’aiki
1. Zaunawa Mufida ta yi a hankali. Maimakon
Mufida ta zauna a hankali.
2. Kallon sa A’isha ta yi a wulaƙance. Maimakon
A’isha ta kalle shi a wulaƙance.
Duk da cewa kalmar ‘zaunawa’ da ‘kallo’ ba su zo da sigar Aikatau ba a cikin jumlolin, sun zo ne a matsayin Suna ɗan’aiki (ɓerbal Noun), amma ba su da muhalli a wuraren da aka saka su. Saboda Suna ɗan’aiki bai kamata ya zo kafin K² ba, watau a matsayin sft¹.
3.1.1 Farawa da Bayanau
1. A hargitse A’isha ta shiga ɗaki. Maimakon
A’isha ta shiga ɗaki a hargitse.
2. A hankali Maryam ta sauke ajiyar zuciya. Maimakon
Maryam ta sauke ajiyar zuciya a hankali.
A misalin jumla ta farko, kalmar ‘A’isha’ (K²) kawai ya kamata a gani a Yankin Suna. Sai kuma kalmomi kamar:
‘ta’ = Zagin Aikatau
‘shiga’ = Aikatau
‘ɗaki’ = Suna (YS²)
‘a hargitse’ = Bayanau
Duka waɗannan a Yankin Aiki/Bayani ya kamata a ambace su.
A misalin jumla ta biyu kuwa, kalmar ‘Maryam’ (K²) kawai ya kamata a ambata a Yankin Suna. Yayin da kalmomi irin su:
‘ta’ = Zagin Aikatau
‘sauke’ = Aikatau
‘ajiyar zuciya’ = Suna ɗan’aiki (YS²) —idan ba a faɗaɗa li’irabi ba.
‘a hankali’ = Bayanau
Waɗannan duk a Yankin Aiki ya kamata a ambace su.
3.2 Warware Bayani
Idan har Aikatau da Bayanau suna zuwa ne a *Yankin Aiki/Bayanau* na jumla, wanda kuma a ƙarshen jumla wannan yanki yake zuwa; to bai kamata a dinga dawo da su *Yankin Suna* wanda ke farkon jumla ba. A nawa hasashen yin haka ɓata tsarin ginin jumla ne ko kuma ɓata ƙa’idar Nahawun Hausa. Ban ƙi ba idan hakan ta zo a cikin rubutun waƙa, Mawaƙi zai iya fakewa da lemar alfarma da masana suka lulluɓa masa na cewa ba za a kama sa da laifin saɓa wa wata ƙa’ida ta Nahawu ba.
4.0 Kammalawa
An yi wannan nazari ne domin yin hannunka-mai-sanda ga wasu marubuta game da bin tsarin ginin jumlar Hausa. Shi ya sa nazarin ya fara taɓo bayani game da ilimin Ginin Jumla (Syntaɗ) da ma’anar jumla gami da karikitan cikinta. Daga bisani sai nazarin ya bayyana inda gizo ke saƙa, ma’ana wurin da matsalar take. Daga ƙarshe sai aka warware bayani domin fahimtar manufa.
Manazarta
Domin manazarta ko gyara ko ƙarin bayani da shawara a tuntuɓi Manazarcin ta hanyoyi kamar haka:
WhatsApp: 07063828558
Email: [email protected]
