20
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci a riƙe asusu guda huɗu na wasu bankuna da aka alaƙanta su da tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, Mele Kolo Kyari bisa zargin badaƙala, makirci, wulaƙanta aiki da sauya akalar wasu kuɗaɗe. Mai Shari'a Emeka Nwite ya yi hukuncin a ranar Talata, ƙarƙashin ƙarar da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati, EFCC ta shigar ta Lauya Ogechi Ujam. Dayake EFCC ta nemi a riƙe asusun na watanni biyu domin ta samu damar kammala bincike akansu, mai shari'ar ya bada kwana 30…
