18
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fasinjar Ibom Air da aka tsare bisa zargin farmakin wanda ya yi ƙoƙarin tsayar da ita a filin jiragen sama, ta musanta shigar da ƙarar Naira biliyan 500 akan Gwamnatin Tarayya da Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama, NCAA. Emmanson ta bayyana haka ne ta kafar Instagram, ranar Asabar. Hakan ya biyo bayan rahoton da ke cewa fasinjar ta wani lauya mai suna Ayodele Ademiluyi, ta shigar da ƙara a wata kotun Legas inda ta nemi a biya ta biliyan N500. Saidai, Emmanson ta nesanta kanta daga lauyan, inda ta ce kawo yanzu ba…
