Babaji

5698 Posts

Yadda gyare-gyaren Tinubu ke inganta tattalin arziƙin Nijeriya – Okonjo-Iweala

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa ƙoƙarinsa na ingantawa da samar tabbatuwa ga harkokin tattalin arziƙi a Nijeriya inda ta ce gyare-gyare da gwamnatinsa ke yi suna tafiyar da ƙasar yadda ya dace. Ta bayyana haka ne a yayin hira da manema labarai jim-kaɗan bayan ganawa da Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Alhamis. Ta ce, tattaunawar da suka yi da shi ta ƙunshi ƙaddamar da shirin na musamman don inganta rayukan mata a Nijeriya ta tsarin tattali na dijital,…
Read More

Hedikwatar Tsaro ta ƙarfafa farautar Turji sa’o’i 24 da kama jagoran ƙungiyar Mahmuda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Alhamis Hedikwatar Tsaron Nijeriya DHQ, ta sanar da cewa ta baza komar kama sanannen jagoran ƴan bindigar nan, Bello Turji, bayan da jami'anta suka kama shugaban ƙungiyar ta'addanci ta Mahmuda, Abubakar Abba. A ranar Laraba aka kama Abba a yankin Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a jihar Neja bayan samun wani rahoton sirri akansa daga Hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS. Ƙungiyar, wanda reshe ne na Boko Haram, ta sha kai munanan hare-hare a sassan jihohin Kwara da Neja. Daraktan yaɗa labaran DHQ, Manjo Janar Markus Kangye a wata hira…
Read More

Ƙungiyar ASUP ta ba Gwamnatin Tarayya makonni uku ta amsa buƙatun mambobinta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Malaman Makaratun Polytechnics ASUP, ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin makonni biyu na ta biya buƙatun da aka nemi ta sauke da ya shafi walwalar ma'aikata. Shugaban ASUP. Shammah Kpanja a yayin wani zama na gaggawa ranar Alhamis a Abuja, ya bayyana mawuyacin halin da lakcarorin poly suke fuskanta duk da cewa gwamnatin ta yi alƙawarin warware matsalolin ƙungiyar da ta gabatar mata. Ya ce, har yanzu hukumar albashi da kuɗaɗen shiga (NSIWC) ba ta a bayyana lokacin da za a fara biyan lakcarorin alawus ɗinsu na karantarwa ba, wanda a cewarsa yana…
Read More

Abinda masu tambayoyi a EFCC suka faɗa mun – Tambuwal bayan fitowa daga hannun hukumar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya magantu game da haɗuwarsa da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, inda ya bayyana cewa babu wani matsin a siyasance ko daga wata cibiya da za ta tsorata shi. Da yake jawabi ga manema labarai a Sakkwato bayan fitowarsa daga komar EFCC, Tambuwal ya ce ganin sa a ofishin hukumar ya faru ne sakamakon gayyatar da ta yi masa a ranar 6 ga watan nan na Agusta. Ya ce, bayan ganawa ta farko a hedikwatar hukumar, an bar shi ya koma gida…
Read More

RTEAN: An dakatar da sakatare yayin zaman gaggawa na majalisar zartarwa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ƙoƙarinta na tabbatar da gaskiya da adalci yayin aiwatar da harkokin shugabanci, Ƙungiyar Ma'aikatan Sufurin Motoci ta Ƙasa RTEAN, ta shaida wa mambobinta cewa majalisar zartarwarta ta gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba, 13 ga watan Agusta, 2025. Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Muhammad Abubakar Bishara ne ya jagoranci zaman a ƙarƙashin tsarin gudanar da ayyukanta. A wata takarda da RTEAN ta fitar, majalisar ta cimma matsaya game da batutuwa akan Babban Sakatarenta, wato Yusuf Ibrahim Adeniyi bayan nazari game da rahoton da aka gabatar a kansa, inda aka gano wasu ayyukansa sun saɓa…
Read More

Tinubu ya yi ganawar sirri da Okonjo-Iweala

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Shugaba Bola Tinubu ya karɓi baƙoncin Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Sun gana ne a birnin tarayyar Nijeriyar akan batutuwan da suka shafi kasuwanci musamman a yadda suka shafi Nijeriya da ma a mataki na ƙasashen duniya. A wata hira da manema labarai bayan kammala zaman, Okonjo-Iweala, wadda ta samu rakiyar Ministar Kasuwanci, Jumoke Oduwole, ta ce sun ziyarci shugaban ƙasar ne don ba shi ba'asi akan wani abin farin ciki, wanda aka samu nasarar cimmawa da taimakon matar…
Read More

Yadda ɗalibin Jami’ar Obafemi Awolowo ya yi ajalin kansa bayan duba sakamakon jarrabawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani ɗalibin aji biyu da ke karatu a tsangayar koyon aikin likitanci a Jami'ar Obafemi Awolo ya halaka kansa, kamar yadda Kakakin jami'ar, Abiodun Olanrewaju ya bayyana a ranar Alhamis. Ɗalibin mai suna Ajibola Ibitayo, ya ɗauki matakin ne bayan duba sakamakon jarrabawarsa a ranar Laraba, inda ya gano cewa sai ya sake maimaita sashi na biyu a wani zangon karatu bayan ya maimaita a zangon da ya gabata. A sanarwar da kakakin ya fitar, an yi zargin ɗalibin, wanda mahaifinsa babban likita ne, da yi wa kansa allura a gidan iyayensa da ke…
Read More

‘Yan dabar Turji sun sake karya alƙawari bayan aikata ta’addanci a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu ƴan bindiga daga dabar shahararren jagoransu, Bello Turji, sun kai sabon hari a Ƙauyen Garki da ke jihar Sakkwato, inda suka yi awon-gaba da mutane 16 da halaka ɗaya da kuma ɗebe dabbobi da dama duk da ikirarin ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da wakilan gwamnati. Rahotanni sun bayyana cewa, harin, wanda ya auku a yammacin ranar Laraba, an yi shi ne ƙarƙashin jagorancin makusancin Turji mai suna Kallamu da ƴan barandarsa. Wani shaida ya ce, ƴan bindigar sun isa yankin ne a adadi mai yawa inda suka ta yin harbe-harbe, kana daga bisani…
Read More

Sakkwato: An kama na’ibin liman bisa zargin haɗa hannu da ƴan bindiga da gano miliyan N47 a asusun bankinsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an tsaro a jihar Sakkwato, sun yi nasarar kama Sirajo Ɗan Liman, wanda na'ibin Liman ne a babban masallacin Juma'a na garin Kangiye da ke Gundumar Atakwanyo a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa bisa zargin sa da haɗa hannu da ƴan bindiga a yankin Tanga. Majiyoyi sun shaida cewa, wasu bayanai na sirri sun nuna cewa na'ibin yana da alaƙa da ƴan bindigar wajen samar musu da babura da wasu kayayyakin aiki da suke amfani da su wajen kai farmaki, yin garkuwa da mutane, sace dabbobi da kutsa wa wasu sassan shiyyar. A cewar jami'an tsaro,…
Read More

A karon farko PSG ta lashe Super Cup bayan doke Tottenham a bugun fenareti

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Paris Saint Germain ta doke Tottenham Hotspur da ci 4 da 3 a bugun 'daga kai sai mai tsaron gida', lamarin da ya ba ta damar lashe Kofin UEFA Super Cup a karo na farko a tarihinta. An tashi wasan ne 2 da 2 bayan da PSG ta farke ƙwallo biyu da Tottenham ta fara zura mata ana ƙasa da mintuna 15 da ƙarƙare wasan. Da fari Spurs ce ta samu damar nasara a wasan, ƙarƙashin sabon kocinta, Thomas Frank, yayin da ta jagoranci wasan da ci…
Read More