
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ƙoƙarinta na tabbatar da gaskiya da adalci yayin aiwatar da harkokin shugabanci, Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Motoci ta Ƙasa RTEAN, ta shaida wa mambobinta cewa majalisar zartarwarta ta gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba, 13 ga watan Agusta, 2025.
Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Muhammad Abubakar Bishara ne ya jagoranci zaman a ƙarƙashin tsarin gudanar da ayyukanta.
A wata takarda da RTEAN ta fitar, majalisar ta cimma matsaya game da batutuwa akan Babban Sakatarenta, wato Yusuf Ibrahim Adeniyi bayan nazari game da rahoton da aka gabatar a kansa, inda aka gano wasu ayyukansa sun saɓa wa ƙa’idodinta.
Akan haka ne bisa la’akari da dokokin nata majalisar ta yanke shawarar dakatar da shi a matsayin sakataren har zuwa lokacin da za a kammala binciken akan lamarinsa.
Saboda haka kuma majalisar ta samar da kwamitin bincike na mutane bakwai don yin bincike mai zurfi akansa.
Barista Samuel Agbede shi ne shugaban kwamitin yayin da Hon. Adamu Zubairu ne sakatare, sannan an ba su wa’adin wata biyu domin miƙa rahoton bincikensu.
Kazalika, jagorancin RTEAN ya kuma jaddada wa al’umma ƙoƙarinsa na cigaba da bin doka da oda da tsayar da gaskiya da adalci gami da ci-gaban harkokin sufurin motoci a Nijeriya.
