13
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Tarayya ta sanya dokar hana samar da sabbin jami'o'i da polytechnic na tarayya da kwalejin ilimi na tsawon shekaru bakwai, domin rage rashin inganci a harkokin gudanarwa da zuƙe asusun ƙasa. An yanke haka ne a yayin zaman Majalisar Zartarwa (FEC) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Laraba. Baya ga haka ne Ministan Ilimi, Dakta Maruf Olatunji Alausa yayin ganawa da manema labarai ya bayyana cewa akwai ƙalubale da dama wajen harkokin gudanarwar makaratun tarayya musamman a rashin wadatattun ababen more rayuwa, maimaita abinda aka jima…
