Babaji

5698 Posts

Shettima ya jagoranci tawagar Shugaban Ƙasa a ta’aziyyar Audu Ogbeh

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Fadar Shugaban Ƙasa a ta'aziyya ga iyalan marigayi tsohon Ministan Noma da Raya Karkara, Audu Ogbeh. Ogbeh, wanda shi ne shugaban jam'iyyar PDP a tsakanin 2001 da 2005, ya rasu ne a ranar Asabar da ta gabata bayan shafe shekaru 78 a duniya. Shettima ya bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasa masu hangen nesa, wanda za a cigaba da tuna irin gudumawar da ya bayar ga harkar tsaron abinci a tarihin raya ƙasa. Ya ce, rashin Ogbeh zai haifar da…
Read More

Sa’o’i bayan naɗa ta, Tinubu ya maye gurbin Dakta Ɗankaka a FCC yayin garambawul ga ma’aikatansa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yayin wani juyin yanayi, Shugaba Bola Tinubu ya tsige Dakta Muheeba Ɗankaka daga muƙaminta na Shugabar Hukumar Tabbatar da Daidaito (FCC), sa'o'i kaɗan da naɗa ta, inda ya maye gurbinta da tsohuwar ƴar majalisa, Ayo Hulayat Omidiran. Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da manema labarai hakan a wata takarda. Omidiran, wadda ƴar majalisar wakilai ce har sau biyu daga jihar Osun, ta maye gurbin Dakta Ɗankaka, wadda aka nuna rashin amincewa da naɗin nata, kamar yadda kakakin ya bayyana. Haka kuma, Tinubu a yayin garambawul ɗin ya naɗa…
Read More

An kama sojojin Mali bisa zargin yunƙurin juyin mulki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni daga Bamako, Babban Birnin ƙasar Mali sun ce an kama sojoji da dama bisa zargin su da shirin kifar da mulkin sojin ƙasar. An yi kamen ne a dare ɗaya wanda kuma ake sa rana cigaba da yi a yayin da jagorancin ƙasar ke fuskantar matsi sakamakon rahotannin ƙamarin rashin tsaro daga arewacin ƙasar. Kawo yanzu hukumomin ƙasar ba su yi tsokaci game da kamen ba. Wani rahoto da BBC ta fitar ya nuna cewa, da fari Janar Abass Dambele, wanda tsohon gwamnan shiyyar Mopti ne da Janar Nema Sagara, ɗaya daga cikin…
Read More

Kaduna: Zanga-zanga ta ɓarke bayan jami’an NDLEA sun harbe na gefen hanya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Litinin al'umma a yankin Barnawa da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu suka shiga mawuyacin hali bayan zargin wasu jami'an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) sun harbe wani matashi. Lamarin da ya haifar da zanga-zanga daga wasu fusatattu tare da cika tituna da rufe wani sanannen wajen shaƙatawa. Wani shaida ya ce, wanda aka harben ya kasance mutum ne kamili kuma jajirtacce wajen nema abincinsa, inda wani alburushi ya same shi bisa kure a yayin da jami'an suke farautar wani dillalin ƙwaya. Al'amarin ya auku ne a yankin madakatar…
Read More

EFCC ta kama Tambuwal kan zargin badaƙalar biliyan N189

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya shiga hannun jami'an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, bisa zargin sa da hannu a badaƙalar wasu tsabar kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 189. Tambuwal, wanda tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ne, ya kai kansa hedikwatar EFCC a Abuja da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Litinin, inda masu bincike suka yi masa wasu tambayoyi. Wani jami'i da ya nemi a sakaye sunansa, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa ana zargin tsohon gwamnan ne da fitar da wasu kuɗaɗen al'umma a zamanin…
Read More

Zamfara: Sojoji sun halaka ƴan bindiga sama da 100 a Bukkuyum

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro sun yi nasarar halaka sama da ƴan bindiga guda 100 a wani luguden wuta ta sama da ƙasa a Jihar Zamfara, kamar yadda rahotanni suka bayyana. An ƙaddamar da mummunan harin ne akan ƴan bindigar a Ƙaramar Hukumar Bukkuyum yayin harin sama da 400 daga cikinsu a dajin Makakkari. Sojojin sama a jiragen yaƙi da suka yi aiki tare da sojojin ƙasa, sun tarwatsa sansanin ƴan ta'addar gabannin kashe waɗanda suka yi yunƙurin tserewa. Ana ganin hakan a matsayin martani ga munanan hare-haren ƴan bindigan akan al'umma da jami'an tsaro musamman a…
Read More

Kaduna: Mutane da dama sun rasu bayan fashewar tankar mai a Zariya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mutane da dama sun rasu yayin da wasu suka jikkata bayan wata tanka maƙare da mai ta fashe a Jihar Kaduna. Lamarin ya auku ne a safiyar yau Litinin kusa da makarantar Rochas Foundation School da ke babban titin Kaduna zuwa Kano a tsakanin Kwangila zuwa Ɗan Magaji dake yankin Zariya. Mai sharhi kan lamuran daƙile ayyukan ta'addanci, Zagazola Makama, ya ce lamarin ya rutsa ne da wasu tankokin mai biyu da motocin Golf biyu da ke cike da fasinjoji. Wani shaida ya ce, a iftila'in an ga fashewar wuta sau biyar tare da…
Read More

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da jita-jitar rashin lafiyar Tinubu

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta rahotannin da ke nuna cewa shugaba Bola Tinubu ba shi da lafiya kuma ana shirin fitar da shi zuwa asibiti a ƙasar waje. A makon da ya gabata ne cibiyar aikin jarida mai binciken ƙwaƙwaf ta Nijeriya, ICIR ta rawaito cewa wasu majiyoyinta sun tabbatar mata da cewa tawagar likitocin shugaban ƙasa na ta shirye-shiryen fitar da shugaba Tinubu zuwa ƙasar wajen domin neman magani. Cibiyar kamar dai yadda ta wallafa a shafinta na intanet ta ce "rahotanni na nuna cewa shugaba (Tinubu) na kwance a gado ba ya iya zuwa ko'ina abin da ya…
Read More

Nazarin sakamako: Masu ruwa da tsaki sun nemi a yi bincike da hukunta masu hannu a faɗuwar jarrabawar WAEC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Masu ruwa da tsaki a fannin ilimi sun sake sukar Cibiyar Gudanar da Jarrabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) bisa sauya sakamakon jarrabawar WASSCE ta 2025. Rahotanni sun bayyana cewa masu ruwa da tsakin a mabanbanta hira da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Abuja, sun nemi a yi bincike mai zurfin akan baki ɗaya hukumar gudanarwar WAEC. Sun ce, ba za a amince da samun kurakurai a jarrabawar kammala sakandare ta ɗalibai ba duba da cewa shi ne abinda zai nuna cancantar su shiga makarantun gaba. Haka kuma, sun bayyana cewa matuƙar za a riƙa…
Read More

Filato: Jami’an tsaro sun kama sojan bogi a Jos

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an sojojin Atisayen SAFE HEAVEN, wato OPSH a Filato, sun yi nasarar kama wani Musa Ali a Jos bisa laifin sojan gona, inda ya yi basaja a matsayin jami'insu. Kakakin jami'an, Manjo Samson Zhakom ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ranar Asabar. Ya ce, an yi nasarar kama wanda ake zargin ne a yayin da ya yi yunƙurin damfarar wasu jama'an gari. Musamman Kakakin ya ce wanda ake zargin ya yi yunƙurin damfarar iyalan wani mai safarar makamai da aka kama da sunan zai musu…
Read More