
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da jami’an tsaro suke ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci a sassan ƙasar, jami’an tsaro a Chadi da Nijeriya sun yi nasarar cafke wasu jagororin mayaƙan ƴan ta’adda da ke ayyukansu a yankin Tafkin Chadi.
Hukumomi a Chadi sun tabbatar da kama wasu mambobin Boko Haram guda shida ciki har wani da matashi mai suna Muslim Mohammed Yusuf da ake kyautata zaton ɗan marigayi Mohammed Yusuf ne, wato wanda ya samar da ƙungiyar.
Hakan ya biyo da gwamnatin Nijeriya ta sanar da kama manyan jagororin tsagin ƙungiyar Ansaru a ƴan kwanakin nan, lamarin da ya sa Amurka ta taya Abuja murna inda ta bayyana hakan a matsayin babbar nasara a faɗa da ta’addanci da tsatstsauran ra’ayi.
Ana tsaka da haka ne ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya sanar tsauraran matakai game da mallakar biza ga ƴan Nijeriya inda daga ciki akwai batun bayyana bayanan kafafen sada zumunta na tsawon shekaru biyar saboda matsalolin tsaro a mataki na duniya.
Wata majiyar sirri da ke aiki a Tafkin Chadi ce ta fara fitar da rahoton kama Muslim Yusuf, wanda ake kira da Abdrahman Mahamat Abdoulaye, wato sunansa da yq shahara da shi acikin mayaƙan.
Majiyar ta kuma ce, an tsare matashin mai shekaru 18 tare da wasu mayaƙa guda biyar a N’Djamena bayan wani artabu da dakarun tsaro.
Haka kuma, hotunan da aka ɗauka bayan kamen sun nuna wani matashi mai sanye da rigar kot launin ɗorowa da kamanni da mahaifinsa a tsaye da sauran waɗanda aka kama su tare.
Yusuf, wanda yaro ne ɗan ƙarami a lokacin da aka halaka mahaifinsa a shekarar 2009 yayin wani rubdugu na sojoji da ya yi sanadin kashe mutane kusan 800, shi ne kuma ƙanin Habib Yusuf (wanda ya shahara da Abu Mus’ab al-Barnawi), wato shugaban mayaƙan ISWAP na yanzu.
