Borno: ‘Yan ƙwadagon gona sun ankarar da ƴan sanda nakiya a Dikwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda a Jihar Borno, ta yi nasarar lalata wata nakiya da aka gano a wata gona samfurin UXO bayan ankarar da su da ƴan ƙwadagon gonar suka yi.

Lamarin ya auku ne a Ƙaramar Hukumar Dikwa wanda ya taimaka wajen kawar da wani mummunan iftila’in da ka iya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

An samu nasarar ne a lokacin da wani manomi mai suna Babagana Kachalla ya ruwaito cewa an binne wani abu da ba su san mene ne ba a gonarsa.

Daga nan ne Kwamishinan ƴan sandan jihar, Naziru Abdulmajid ya baza jami’an lalata boma-bomai (EOD) na shiyya ta 13 a Maiduguri zuwa wajen.

A sanarwar da Kakakin ƴan sandan, ASP Nahum Daso ya fitar, ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya ce sun gano an binne nakiyar da ke da tsawon mita 2.2 da faɗin santimita 30.

Ya kuma ce, an yi nasarar lalata ta ba tare da samun tsaiko ba a yayin haka.

Daga nan ne jami’an suka shiga cikin garin inda suka wayar da kan al’umma akan yadda za su gano ababen zargi musamman waɗanda ke da alaƙa da na fashewa.

Kazalika, ya kirayi al’umma da su kasance masu kula da gaggauta ruwaito wa hukuma dukkan wani abin zargi da suka gani a yankunansu.

By Babaji