Talakawa miliyan 2.2 za su samu tallafin Gwamnatin Tarayya, inji minista

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Litinin Ministan Jinƙai, Tanko Sununu ya ce Gwamnatin Tarayya tana aiki tuƙuru wajen kawo ƙarshen talauci acikin al’ummar Nijeriya.

A wata hira da gidan talabijin na Channels, Sununu ya bayyana cewa sama da magidanta miliyan biyu ne aka tantance waɗanda nan ba da jimawa ba za su samu tallafin kuɗaɗe daga gwamnati.

“Nan da ƴan kwanaki kaɗan, kafin ƙarshen Agusta, za mu kai ga magidanta miliyan 2.2.”

Ministan ya ƙara da cewa, gwamnatin tarayya ta samar da shirye-shirye da dama domin tallafa wa talakawa da marasa galihu a ƙasar.

Sununu ya kuma ce, an samu nasar a shirin tura kuɗaɗe zuwa asusun bankuna na CCT, inda tuni aka raba biliyan N419 ga ƴan Nijeriya su guda miliyan biyar.

“Mun raba kaso 71 a ɓangaren arewa, sannan kaso 21 a ɓangaren kudancin ƙasar”, inji Ministan.

By Babaji