
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kebbi a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2019, Sanata Isa Galaudu ya sanar da barin jam’iyyar.
Galaudu, wanda ya taɓa zama shugaban ma’aikata na tsohon shugaban Majalisar Dattawa, ya sanar da haka ne a wata takarda da ke ɗauke da 20 ga Agusta a matsayin kwanan wata, sannan ya aika ta zuwa ga shugaban jam’iyyar na Gundumar Augie a jihar.
Ya bayyana cewa, ficewarsa daga jam’iyyar za ta fara aiki ne a nan take.
Haka kuma, tsohon ma’aikacin na banki kuma tsohon ɗaya daga cikin jagororin Jami’ar Usman Ɗanfodiyo ta Sakkwato, ya ce ya ɗauki matakin ne duba da yadda jam’iyyar ta ɗauko hanyar durƙushewa.
Sanata Galaudu, ya wakilci yankin Kebbi ta Arewa a Majalisar Dattawa tsakanin 2011 da 2015, sannan ɗan takarar gwamna ne a zaɓen 2019 a jihar Kebbi.
