
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen ƙasa (NRC) ta dakatar da zirga-zirga a Abuja zuwa Kaduna bayan gocewa da wani jirgi da ke ɗauke da fasinjoji ya yi daga hanyarsa a safiyar yau Talata, lamarin da ya yi sanadin raunata mutane shida.
Hakan ya faru ne da misalin ƙarfe 11 bayan jirgin ya tsahi daga Abuja da nufin zuwa Kaduna, inda fasinjojin da ke cikinsa suka razana tare da ficewa daga ciki saboda tsoron kai musu farmaki.
Da yake ganawa da manema labarai, Darakta Manaja na NRC, Kayode Opeifa ya ce dakatarwar za ta cigaba da aiki ne har zuwa lokacin kammala bincike akan al’amarin.
Sannan, ya tabbatar da cewa mutane uku sun samu ƙananan raunuka kuma ana ba su kulawa.
Haka kuma ya bayyana cewa ba a iya ƙididdige adadin fasinjojin da ke cikin jirgin ba a lokacin da abin faru.
Kazalika, shugaban hukumar ya yi watsi da jita-jitar da ke cewa al’amarin ya faru ne sakamakon rashin kula da jiragen yadda ya dace, yana mai cewa sun ɗauki matakin ne domin kauce wa aukuwar irin haka a nan gaba.
Tuni Cibiyar Binciken Kariya ta Ƙasa (NSIB) ta sanar da aika tawaga ta musamman zuwa wajen da abin ya faru domin gano musabbabin faruwarsa.
