Masarautar Daura ta gudanar da bikin Ranar Hausa ta duniya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Masarautar Daura a Jihar Katsina ta gudanar da gagarumin bikin ranar Hausa ta duniya domin ƙarfafa harshen Hausa da ɗaukaka harshen Hausa da kuma al’adun Hausawa.

Taken ranar Hausawa an sa mata suna “Al’adun mu jiya,yau da gobe,”ya gudana a fadar mai martaba Sarkin Daura Umar Farouk Umar.

Masu riƙe da sararin gargajiya, makaɗa da waƙe waƙe da maza da mata da kuma mahaya dawaki da suka zo daga sassa daban daban daga ciki da wajan jihar da kuma suka halarci bikin.

Muƙaddashin Gwamnan wanda ya sami wakilcin mai ba gwamna shawara kan masarautu Usman Abba Jaye, ya yabawa Sarkin Daura da ya ɗauki nauyin wannan biki mai ɗimbin tarihi.

Ya bayyana mahimmancin rawar da al’adun Hausawa ke takawa wajen zaman lafiya da haɗa kan al’umma.

Abba Jaye ya bada tabbacin cewa gwamnati za ta taimaka wajen ɗaukaka al’adun Hausa wanda shine haɗa kan al’ummar Hausawa tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Firaministan ƙasar Nijar Ali Laminu Zain da ya wakilci gwamnan Zander Muhammad Umar ya yaba wa Sarkin Daura bisa wannan gajiya da yayi masa.

“Duk lokacin da ɗan ƙasar Nijar ya ganshi a Nijeriya sai yaga kaman yana gida haka shima ɗan Nijeriya ya shiga ƙasar Nijar sai ya ji kamar yana ƙasar Nijeriya,”inji kanal Umar.

Shima da yake jawabi wazirin Katsina sanata Ibrahim Ida ya sanar da cewa akwai Hausawa guda miliyan 200 a faɗin duniya.

Matasa daga ko ina a Arewacin kasar nan da ƙasar Nijar suka halarci bikin tare da gudanar da sukuwa domin girmama Sarkin Daura da sauran sarakuna da suka halarci bikin.

By ukarofi