Mai juna biyu da wasu sun rasu a kogo yayin haƙar ma’adanai a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani yanayin na jimami a garuruwan jihohin Neja da Filato, an yi rashin mutane da dama a wuraren haƙar ma’adanai ta haramtattun hanyoyi a sanadiyyar ruftawar ƙasa da tarwatsewar ababen fashewa.

Rahotanni sun bayyana cewa wani iftila’i ya rutsa da mata biyar da suka gamu da ajalinsu ciki har da mai ciki a yayin da suke tsaka da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida a Ƙaramar Hukumar Paikoro ta jihar Neja, a yammacin ranar Talata.

Mamatan sune: Tani Abubakar (mai juna biyu), Farida Mustapha, Farida Sule, Khadijat Abdullahi, da Zainab Usman, waɗanda dukkan su ƴan ƙauyukan Budu da Panbi ne.

Tuni jami’an hukumomin bada agajin gaggawa suka garzaya wajen da abin ya faru tare da zaƙulo gawawwakin da kai su babban asibitin Paikoro inda aka tabbatar da mutuwarsu.

Tun a baya hukumomi suka sha gargaɗin mutane game da yin ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba duba da yadda hakan ke zama barazana ga rayuka da tattalin arziƙin ƙasa.

A watanni kaɗan da suka gabata makamanci haka ya faru a Sabon Pegi da ke Ƙaramar Hukumar Mashegun a jihar, wanda ya yi sanadin rasa rayuka biyu da lalata wasu gine-gine da gidaje da adadinsu ya kai guda 20.

A cewar Ministan Ma’aikatar Ci-gaban Albarkatun Ƙasa, Dele Alake, bincike ya nuna cewa wani mazaunin yankin New Bussa mai suna Yushau Maikampala ne ya dasa wasu ababen fashewar da suka yi sanadin iftila’in, wanda ake zargin sa da hannu a sayen kayayyakin fashewa na haƙar ma’adanai ta haramtattun hanyoyi, kamar yadda mai taimaka masa akan yaɗa labarai, Segun Tomori ya bayyana a wata takarda.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda iftila’in ya rutsa da su, yana mai jaddada gargaɗin gwamnatin ga masu mallakar ababen fashewa ta haramtattun hanyoyi.

Haka ma a Ƙaramar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato, inda aƙalla mutane 13 suka rasu yayin da ƙasa ta rufta musu a lokacin da suke aikin haƙar ma’adanai a farkon wannan shekarar.

By Babaji