DSS ta nemi kotu ta karɓi rahoton ƴan leƙen asirin Iran a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar ƴan sandan farin kaya DSS, ta buƙaci Babbar Kotun Tarayya ta Abuja da ta karɓi rahoton mutane uku da ake zarginsu da leƙen asiri a Nijeriya ga Amurka da Isra’ila a madadin wasu ƴan Iran.

Waɗanda ake zargin sune Haruna Ali Abbas, Ibrahim Hussaini Musa da Adam Suleiman waɗanda aka kama su a Kano da Legas tun a 2013 inda daga bisani aka maka su a kotu bisa laifuka masu alaƙa da ta’addanci.

An zarge su ne da ayyukan ta’addancin da ake zargin ana gudanar da su ne ƙarƙashin wani iko daga Iran.

A yayin shari’ar a ranar Laraba, lauyan da ke kare ɓangaren masu ƙara, Bello Abu, ya roƙi Alƙali Emeka Nwite da ya karɓi rahoton da ɓangaren nasa ya gabatar sakamakon ƴan ɗaya ɓangaren sun yi ikirarin an tilasta mutane ukun da amsa abinda ake zargin su a kai, lamarin da a cewarsa ƙoƙari ne na dagula al’amuran shari’ar.

Saidai, ƴan ɗaya ɓangaren, wanda akwai lauya Aliyu Yawuri, Bala Dakun da Bello Ibrahim, sun yi wa kotun magiya da cewa kada ta karɓi rahoton kalaman duba da cewa ba da raɗin kai aka gina su ba.

Daga cikin ababen da DSS ta gabatar akwai cewa Abbas, wanda ɗaya ne daga cikin waɗanda ake zargin, yana halartar taron ƴan ta’adda sannan yana taimakawa ta hanyar tura mambobi zuwa Iran domin koyo horon yadda ake gudanar da ta’addanci.

By Babaji