Babaji

5698 Posts

Odeh da Adewunmi sun zama jagororin yaɗa labarai a NNPC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, ya sanar da naɗin ƙwararru biyu, wato Andy Odeh da Misis Morenike Adewunmi a wasu manyan muƙamai da nufin inganta harkokinsa. An naɗa Odeh ne a matsayin Shugaban harkokin yaɗa labarai yayin da Misis Adewunmi kuma ta zama babbar jami'ar hulɗa domin gudanar da ɓangaren hulɗa da jama'a da samar da dabarun gudanarwar harkokin masu ruwa da tsaki. Ana sa ran Andy Odeh, wanda ke da ƙwarewa na tsawon sama da shekaru talatin a fannonin sadarwa, talla da masana'antar mai da gas, zai bada gagarumar gudumawa ga…
Read More

Ƙungiyar Kansilolin APC ta jinjina wa Gwamnan Kebbi kan biyan tsofaffin kansiloli haƙƙinsu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar kansilolin jam'iyyar APC ta ƙara NPCF, ta yaba wa Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu bisa karamcinsa na sahale wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai biliyan N2.185 don kammala biyan dukkanin bashin da tsoffin kansilolin jihar tun daga zangon 2004 zuwa 2024 suke bin gwamnati. Ta bayyana shi a matsayin shugaba mai tsananin tausayi bisa share kukan waɗannan bayin Allah game da haƙƙoƙinsu na tsawon sama da shekaru 20. Hon Muslihu Yusuf Ali, a wata takarda, ya kuma taya ƴan jihar kebbi murnar manyan ayyukan alheri da na more rayuwa da…
Read More

Tinubu ya dawo da Shugaban NTA kan muƙaminsa mako guda da sauke shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci a dawo da Salihu Abdullahi Demos kan muƙamin darakta-janar na gidan talabijin na NTA a yau Talata. Dembos ya bar muƙamin ne a kwanan nan bayan wasu ƴan gyare-gyare da aka yi wa hukumar gudanarwar gidan talabijin ɗin. A watan Oktoban 2023 Shugaba Tinubu ya naɗa Dembos a muƙamin, inda a yanzu zai dawo domin kammala wa'adinsa na shekara uku. Kamar haka ne Shugaban Ƙasar ya umarci a dawo da Ayo Adewuyi, wato daraktan yaɗa labarai kan muƙaminsa domin cika zangonsa na shekara uku, wanda zai ƙare a 2027.…
Read More

Yadda ƴan dabar siyasa suka farmake ni a Kebbi – Malami

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya yi zargin wasu ƴan dabar siyasa sun farmaki tawagar motocinsa a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi. A wata sanarwa da ya fitar yau Talata, Malamin ya bayyana al'amarin a matsayin abin takaici a tarihin siyasar jihar, inda ya zargi wasu manyan mutane a jihar da ɗaukar nauyin harin. Ya ce, al'amarin ya auku ne a ranar Litinin a lokacin da ya ke dawowa daga ziyarar ta'aziyya ga Sarkin Gwandu da iyalan marigayi Imam Tukur Kola. A cewarsa, lamarin ya faru ne gidansa da ke…
Read More

Ranar haihuwa: Remi Tinubu ta bada asusun banki don tara mata kuɗin gina ɗakin karatu na ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Matar Shugaban Ƙasa Oluremi Tinubu ta yi magiya ga ƴan Nijeriya da su bada gudumawar zagayowar ranar haihuwarta don tallafa wa aikin gina ɗakin karatu na ƙasa. Tsohuwar sanatar, wadda za ta cika shekaru 65 a ranar 21 Satumba, 2025, ta bayyana haka ne ta wani faifan bidiyo, inda ta ce za ta sadaukar da ranar zagayowar haihuwar ne ga ubangiji a madadin yin biki na musamman domin sa. Don haka ta roƙi al'ummar Nijeriya da su aika mata da gudumawarsu ta kuɗi a madadin katina, wainar fulawa, fulawa ko gaisuwa a jarida da…
Read More

Hedikwatar Tsaro ta magantu kan zargin ba ƴan bindiga kuɗaɗen fansa da alawus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojojin Nijeriya ta nesanta kanta daga zargin cewa tana bai wa ƴan bindiga kuɗaɗe, lamarin da ta ƙaryata da babbar murya inda ta ce ba ya daga cikin salonta biyan kuɗin fansa ko alawus gare su a kowane wata wajen daƙile ayyukan ta'addanci. Shugaban tsaro na gudanarwa, Manjo Janar Emeka Onumajuru ya faɗi haka a yau Talata yayin hira da gidan talabijin na Channels. Ya bayyana cewa, biyan kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ƴan ta'adda abu ne da ke ƙara musu karfi a madadin daƙile ayyukansu na ta'addanci. Ya kuma ce, a madadin haka rundunar…
Read More

Ku fice kafin bizarku ta ƙare ko a kore ku – Hukumomin Birtaniya ga ɗaliban ƙasashen waje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dubunnan ɗaliban ƙasashen waje ciki har da ƴan Nijeriya da dama da ke karatu a Birtaniya ne aka bai wa gargaɗin ficewa daga ƙasar da zarar bizarsu ta ƙare ko kuma a kore su. A cewar wani rahoto daga BBC a ranar Talata, ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta fara aika wa ɗalibai saƙonni ta wayoyin hannunsu na tunatar da su game da dokokin shige da fice. Lamarin na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumomin ƙasar suka koka game da yawaitar adadin ɗaliban da wa'adin bizarsu ta ƙare kuma suke cigaba da…
Read More

Za a gyara layin dogo na Abuja zuwa Kaduna a kwana 10, inji Ministan Sufuri

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Sufuri, Sa'idu Ahmed Alƙali ya tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa nan ba da jimawa ba za a gyara wuraren da suka lalace na layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata. Lamarin ya auku ne sakamakon gocewa da wani jirgin ƙasa da ya yi jigilar mutane daga Abuja ya yi, inda ya nufi Kaduna a ranar Talata. Duk da cewa da dama daga cikin fasinjojin sun tsira, guda bakwai daga ciki sun samu raunuka, inda aka garzaya da su asibiti jim-kaɗan bayan faruwar al'amarin. Da yake jawabi a wajen da…
Read More

Ban yi kuskuren ɗaukar ka mataimaki ba – Tinubu ga Shettima yayin zagayowar ranar haihuwarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yanayi na karramawa, Shugaba Bola Tinubu ya taya Mataimakinsa, Kashim Shettima murnar cikar sa shekaru 59 a duniya. Tinubu ya bayyana Shettima a matsayin mataimaki mai biyayya da ya cancanci a dogara da shi wajen sauke nauyin hidimta wa al'umma da ma ƙasa baki ɗaya. A sanarwar da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce bai yi kuskure ba wajen zaɓar Shettima a matsayin abokin tafiyarsa, wanda kuma ya zama mataimaki a gare shi wajen shugabantar Nijeriya. Ya jinjina wa jajircewar Shettima da ƙoƙarinsa wajen samar da haɗin kai…
Read More

Likitoci sun ba Gwamnatin Tarayya kwana 10 ta amsa buƙatunsu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Likitoci Masu karɓar horo ta Ƙasa NARD, ta ce a shirye ta ke ta tsunduma cikin yajin aiki duba da yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza biyan buƙatunta. Saboda haka likitocin ƙungiyar suka ba gwamnatin wa'adin kwanaki 10 na ta warware musu buƙatun ko kuma su shiga yajin aiki a baki ɗaya sassan ƙasar. NARD ta bada gargaɗin ne a wata takarda ƙarƙashin majalisar zartarwarta a ranar Lahadi, inda ta ce ta yi haka ne sakamakon jinkiri da ake cigaba da samu wajen warware matsalolin walwalarsu. Daga cikin buƙatun akwai gaggauta biyan su kuɗin…
Read More