05
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Kaduna, ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa'i da wasu jiga-jigan jam'iyyar ADC bisa zargin su da hannu a ƙulla makirci da ta da zaune-tsaye acikin al'umma. A cewar rundunar ƴan sandan ta Mataimakin Kwamishinsu a jihar ɓangaren Cibiyar Bincike CID, Uzainu Abdullahi, an ba da takardar ne a ranar 4 ga Satumba, 2025. A ciki an nemi El-Rufa'i da wasu mutane biyar da su je ofishin hukumar reshen CID a ranar 8 ga watan domin amsa tambayoyi nasu alaƙa da zarge-zargen da ake musu. Sauran waɗanda aka gayyato…
