06
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dokokin Jihar Filato ta haramta tilasta saya wa ɗalibai litattafai a kowace shekara a makaratun da ke faɗin jihar, lamarin da a cewarta ke zama matsi ga iyayen yara. Hakan na zuwa ne a lokacin da Hon. Joseph Bukar na mazaɓar Shandam ya ɗauki nauyin ƙudirin inda ya samu goyon bayan Hon. Mathew Kwarpo Sylvanus na Mangun ta Kudu a yayin zaman Majalisar a Jos. Hon. Bukar ya koka kan yadda hakan ke takura wa iyayen yara masu zuwa makaranta a kowace shekara yayin da na baya suna nan da kyansu, lamarin da…
