Babaji

5698 Posts

Rikicin Kwankwasiyya: NNPP ta kori Hon. Abdulmumin Kofa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta sanar da sallamar Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa mai wakiltar mazaɓar Ƙiru/Bebeji a Majalisar Wakilai daga cikin jam'iyyar sakamakon ƙamarin rikicin cikin gida. Hakan na zuwa ne yayin da ta zargi ɗan majalisar da yi wa jam'iyyar zagon-ƙasa, rashin biyayya da gaza sauke nauyin kuɗin jam'iyyar akansa. Da yake ganawa da manema labarai a Kano, Shugaban jam'iyyar Hashim Sulaiman Dungurawa ya bayyana sukar jam'iyyar a fili da rikici tsakaninsa da takwarorinsa na siyasa ya sa NNPP ta ɗauki matakin akansa. Hakan ya faru ne ƙasa da sa'o'i 24 da…
Read More

Edo: ‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da ɗan Chana bayan halaka jami’an Cibil Defens 8

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An sace wani ɗan Chana bayan kashe jami'an Hukumar Cibil Defens (NSCDC) su guda takwas a yankin Okpella da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Kudu a Jihar Edo. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kuma raunata wasu jami'an NSCDCn guda huɗu da wani farin hula, waɗanda suke karɓar a wani asibiti. Lamarin ya auku ne a lokacin da jami'an hukumar da aka tura aiki a kamfanin siminti na BUA da ke jihar ke rakiyar wasu ƴan Chana biyar bayan dawowa daga sintiri, a bakin shiga farfajiyar kamfanin. Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa…
Read More

An garzaya da kocin PSG asibiti bayan hatsari ya rutsa da shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An garzaya da kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, Luis Enrique zuwa asibiti bayan allon kafaɗarsa ta karye a wani mummunan hatsari da ya rutsa da shi. PSG ta tabbatar da faruwar al'amarin a sanarwar da ta wallafa ta kafar X, inda ta ce ɗan Sifaniyar kocin mai shekaru 55 da ya jagoranci ƴan wasanta a lashe kofin Champions League, za a masa aiki bayan samun raunin a ranar Juma'a. Tuni jami'an bada agaji gaggawa suka fara ba shi kulawa gabanin zuwa asibitin, inda za yi masa aikin gyaran karayar ƙashin kafaɗar nasa. Ta…
Read More

‘Ku manta da kukan ƙaryarsa’: Gwamnatin Inugu ta zargi shugaban kamfanin Sujimoto da hannu a badaƙalar Naira 5.7bn

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Inugu ta zargi shugaban kamfanin Sujimoto Luxury Construction Limited, Olasijibomi Ogundele da damfarar jihar Naira biliyan 5.7 da aka biya na kwangilar gina makarantun Smart Green guda 22 a jihar. Kakakin Gwamna Peter Mba ya sanar da haka a ranar Juma'a. Da fari, Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta sanar da neman Ogundele ruwa-a-jallo bisa zargin sa da sauya akalar kuɗaɗen gwamnati. Sa'o'i kaɗan da haka ne aka gan sa a wani faifan bidiyo yana zubar da ƙwalla tare musanta zargin da ake yi masa akan al'amarin. A…
Read More

Rundunar soja ta gargaɗi al’umma kan shafin ɗaukar aiki na bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojojin Nijeriya NA, ta fitar da saƙon ankarar da al'umma game da wani shafin ɗaukar aiki na bogi da aka buɗe da sunanta, cewa an fara ɗaukar ƙananan sojoji aiki a karo na 90. Daraktan hulɗa da jama'a na ofishin ɗaukar aikinta, AU Hammanga ya ce shafin da ake yaɗawa na bogi ne domin a ruɗar da al'umma don haka ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da shi. Rundunar ta bayyana cewa za a samu sahihin shafin ɗaukar aiki ne daga kafafen labarai da ta amince da su, inda za…
Read More

Babban Hafsan Tsaro ya taya sojoji murnar Maulidi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Hafsan Tsaron Nijeriya CDS, Janar Christopher Musa, ya miƙa saƙon taya murna ga jami'an sojoji da ke bikin Maulidi a faɗin Nijeriya. A sanarwar da Daraktan yaɗa labarai na Hedikwatar Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, Janar Musa ya yi kira ga dakarun da su yi amfani da lokacin wajen ƙarfafa haɗin kai, ƙoƙari da biyayyarsu wajen yi ƙasa hidima. Ya ce, kasancewar Maulidi lokaci ne na bikin zagayowar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW, hakan kuma dama ce ta karrama rayuwarsa gami da koyi da karantarwarsa domin samun albarka a rayuwar…
Read More

Rashin tsaro: APC a Zamfara ta zargi Gwamna Lawal da yi wa Gwamnatin Tarayya zagon-ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC a Jihar Zamfara, ta zargin Gwamna Dauda Lawal na jihar da yin ayyukan zagon-ƙasa ga ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na daƙile ta'addanci a jihar. Sakatarenta Yusuf Idris a wata takarda, ya bayyana cewa APC ta nuna damuwa akan kalaman gwamnan na cewa yana sane da zirga-zirgar kowane jagoran ƴan bindiga da sansanoninsu a jihar. APC ta koka kan yadda gwamnan ya ƙi yaƙar su ko bada bayanan sirri ga hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen matsalar duk cewa yana da bayanai akansu. Akan haka ta zarge shi da bai wa ƴan bindiga mafaka a…
Read More

Shirin zanga-zanga: ‘Yan sanda sun ƙarfafa tsaro a ofishin EFCC na Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano ta ƙara adadin jami'an da ke bada tsaro a ofishin hukumar EFCC na jihar sakamakon shirin gudanar da zanga-zanga daga wasu ƙungiyoyin al'umma. A safiyar ranar ne mambobin ƙungiyoyin suka cika a farfajiyar hukumar ta Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati domin nuna goyon baya ga binciken da EFCC da ICPC suke yi akan zargin wasu jami'an gwamnatin jihar da hannu a rashawa. Da yake magana yayin ganawa da manema labarai shugaban tafiyar, Ambasada Abdullahi Muhammad ya ce suna gangamin ne domin ƙarfafawa da…
Read More

Adadin masu neman rijistar jam’iyya a Nijeriya sun kai 171

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe INEC, ta ce adadin ƙungiyoyin siyasa da ke neman a yi musu rajistar jam'iyya sun kai guda 171 zuwa yanzu. A sanarwar da ta fitar ta hannun babban jami'inta na wayar da kan masu zaɓe, Sam Olumekun a ranar Alhamis, inda ya ce daga lokacin da suka bada ba'asi a baya zuwa yanzu an samu ƙarin wasu guda 19 da ke neman a yi musu rajistar jam'iyya. Lamarin da ya sa adadin ya kai 171 a shafin yanar gizo INEC da wasu kafafen yaɗa labarai. A yanzu, INEC tana aiki kan tantance…
Read More

NRC ta dakatar da ayyukan layin dogo na Fatakwal zuwa Aba domin gyare-gyare

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Tashoshin Jiragen ƙasa NRC, ta dakatar da aikin jigilar fasinjoji a layin dogo na Fatakwal zuwa Aba domin gudanar da wasu gyare-gyare. A wata sanarwa daga Darakta-Manajanta, Kayode Opeifa ranar Alhamis, NRC ta tabbatar da batun inda ta ce sun yi haka ne na ɗan lokaci domin tabbatar da bada kulawa yadda ya dace ga harkokin jiragen tashar. Matakin ya sanya ɗaruruwan mutane da ke zirga-zirga ta tashar cikin rashin sufuri a layin, wanda hakan ya sa za su fuskanci matsin tsadar kuɗin wasu ababen hawa. Ya kuma ce, nan da…
Read More