Babban Hafsan Tsaro ya taya sojoji murnar Maulidi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya CDS, Janar Christopher Musa, ya miƙa saƙon taya murna ga jami’an sojoji da ke bikin Maulidi a faɗin Nijeriya.

A sanarwar da Daraktan yaɗa labarai na Hedikwatar Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, Janar Musa ya yi kira ga dakarun da su yi amfani da lokacin wajen ƙarfafa haɗin kai, ƙoƙari da biyayyarsu wajen yi ƙasa hidima.

Ya ce, kasancewar Maulidi lokaci ne na bikin zagayowar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW, hakan kuma dama ce ta karrama rayuwarsa gami da koyi da karantarwarsa domin samun albarka a rayuwar yau da kullum.

Babban Hafsan ya kiraye su da su kasance masu ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da sadaukarwa yayin sauke nauyinsu wajen yi wa al’umma da ƙasa hidima.

Kazalika, ya tabbatar wa al’umma cewa dakarun tsaron ƙasar za su cigaba da aiki tuƙuru wajen ganin an samu haɗin kai da zaman lafiya mai ɗorewa acikin al’umma.

Haka kuma, kamar yadda Annabi Muhammad SAW ya zama abin koyi wajen bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma tsaro, za su cigaba da ƙoƙarin tabbatar da bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma tsaro kamar yadda dokar ƙasa ta tanada.

By Babaji