JIBWIBS ta sanar da rufe masallacin juma’a na Kankiya a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamitin masallacin juma’a na kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa Ikamatul Sunnah ta sanar da rufe masallacin da ke garin Kankiya sakamakon ambaliyar ruwa da ya mamaye masallacin.

Masallacin da ke unguwar Layi quaters ya kai shekara 40 da tubawa,kuma wannan shine karo na farko ya fuskanci wannan iftala’i.

Mai magana da yawun kwamitin Sheikh Khalid Kashim ya bayyana cewa yanzu za a rinƙa gudanar da sallar juma’a a Masallacin Masjid ibn Taymayya a unguwar Gurara.

Ya ce sakamakon ambaliyar ruwa an dakatar da gudanar da salla a masallacin har sai wani lokaci.

Sheikh Kashim ya bayyana cewa wannan mataki da aka cimma ya biyo bayan taro na musamman da ya gudana tsakanin babban limamin masallacin Imam Malam Tasi’u da shugaban kwamitin masallacin Alkasim Rabi’u.

Ya ce wannan mataki da aka ɗauka ya biyo bayan shawara ne da wani ƙwararren injiniya ya bada na rufe masallacin.

Kwamitin na ƙoƙarin ganin ta fara tunanin gina wani masallacin juma’a a garin.

An sami tsawon shekaru 40 kafin a sami irin wannan iftala’i a garin kankiya.

By ukarofi