Rashin tsaro: APC a Zamfara ta zargi Gwamna Lawal da yi wa Gwamnatin Tarayya zagon-ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, ta zargin Gwamna Dauda Lawal na jihar da yin ayyukan zagon-ƙasa ga ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na daƙile ta’addanci a jihar.

Sakatarenta Yusuf Idris a wata takarda, ya bayyana cewa APC ta nuna damuwa akan kalaman gwamnan na cewa yana sane da zirga-zirgar kowane jagoran ƴan bindiga da sansanoninsu a jihar.

APC ta koka kan yadda gwamnan ya ƙi yaƙar su ko bada bayanan sirri ga hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen matsalar duk cewa yana da bayanai akansu.

Akan haka ta zarge shi da bai wa ƴan bindiga mafaka a jihar da barin su suna kashe waɗanda ba su ji ba ba su gani ba da yin garkuwa da mutane.

A wata hira da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, Gwamna Lawal ya shaida musu cewa ya san dukkan sansanoni da zirga-zirgar ƴan bindigar da ke ta’addanci a Zamfara.

Lamarin da ya sa APC ta zarge shi da yunƙurin amfani da hakan wajen samun nasara akan abokan hamayyarsa a siyasa musamman APC a jihar.

By Babaji