Shirin zanga-zanga: ‘Yan sanda sun ƙarfafa tsaro a ofishin EFCC na Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano ta ƙara adadin jami’an da ke bada tsaro a ofishin hukumar EFCC na jihar sakamakon shirin gudanar da zanga-zanga daga wasu ƙungiyoyin al’umma.

A safiyar ranar ne mambobin ƙungiyoyin suka cika a farfajiyar hukumar ta Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati domin nuna goyon baya ga binciken da EFCC da ICPC suke yi akan zargin wasu jami’an gwamnatin jihar da hannu a rashawa.

Da yake magana yayin ganawa da manema labarai shugaban tafiyar, Ambasada Abdullahi Muhammad ya ce suna gangamin ne domin ƙarfafawa da nuna goyon baya ga hukumomin.

Ya kuma ce, hakan wani mataki ne a ƙoƙarin tabbatar da daƙile ayyukan da suka shafi rashawa a faɗin jihar da tsayar da gaskiya da adalci.

Daga cikin al’amuran zarge-zargen akwai na kwanan nan da ake yi akan wasu jami’an gwamnatin jihar da suka haɗa da badaƙalar Naira biliyan 6.5, badaƙalar kamfanin magani na Novomed, rashawa a kayan tallafin da gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin kuɗi na N50,000 ga mata

Kazalika, ya yi tir da da cin zarafin ƴan jarida da wasu jiga-jigan ƙungiyoyin al’umma daga gwamnatin jihar.

By Babaji