Babaji

5698 Posts

DSS ta nemi X ta gaggauta rufe shafin Sowore kan sukar Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta buƙaci hukumar gudanarwar kafar X da ta gaggauta rufe shafin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore. A wata takardar koke da hukumar ta aike wa X, ta buƙaci a rufe shafin nasa a cikin sa'o'i 24. Wani mai suna B. Bamigboye a madaɗin shugaban DSS, ya bayyana cewa matuƙar ba a rufe shafin ba, to za a ɗauki matakin doka a kai. Ya ce, rubutun da Sowore ya yi game da Shugaba Bola Tinubu a ranar 25 ga watan Agusta kai iya haifar da hargitsi a…
Read More

NCoS ta yi alƙawarin miliyan N5 ga wanda ya taimaka aka kamo fursunonin da suka tsere

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Gidajen Gyaran Hali NCoS, ta fitar da bayanan fursunonin da suka tsere daga gidajen yari biyu, wato na Keffi a jihar Nasarawa da Ilesa a jihar Osun yayin da lamuran fashin magarƙama ya fara yawaita a Nijeriya. NCoS ta fitar da bayanan fursunonin ne, waɗanda galibinsu munanan laifuka suka aikata da suka haɗa da fashi da mallakar makamai ba bisa doka ba. A safiyar Talata, 12 ga watan Agusta, fursunoni 16 suka tsere daga kurkukun Keffi da ke Nasarawa bayan sun banƙara jami'an tsaron gidan. A cewar sanarwar da Kakakin NCoS,…
Read More

PETROAN da IPMAN sun nemi Fadar Shugaban Ƙasa ta tsoma baki a rikicin Matatar Ɗangote da NUPENG

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɓangarorin raba man fetur a Nijeriya na fuskantar ƙalubale yayin da Ƙungiyar Ma'aikatan Fetur da Iskar Gas (NUPENG) ta yi barazanar tafiya yajin aiki. NUPENG a wata sanarwa, ta bayyana cewa mambobinta za su tsunduma yajin aiki a daga ranar 8 ga watan Satumba domin nuna ƙiyayyarsu ga rashin kiyaye haƙƙoƙinsu a Matatar Ɗangote. Tuni ƙungiyoyin ƴan kasuwar fetur da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) suka nemi gwamnatin tarayya ta tsoma baki a al'amarin. Hakan na zuwa ne a lokacin da Kamfanin Ɗangote ya shirya raba tirelolin iskar gas (CNG) guda 4,000 ga ƙananan…
Read More

Putin na ƙara matsa wa Ukraniya yayin harin dakarun ƙasashen waje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya yi gargaɗin cewa abin harin dakarun sojojinsa na Moscow a yanzu su ne sojojin ƙasashen Yamma da aka tura su zuwa Ukraniya. A ranar Alhamis, ƙasashe 24 ƙarƙashin jagorancin Faransa da Birtaniya suka nemi a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bisa tsarin da Rasha ta bayar a 2022. Dubunnan mutane yaƙi tsakanin Rasha da Ukraniya ya yi sanadin mutuwarsu yayin da ya ɗaiɗaita miliyoyi da lalata gidaje a gabas da kudancin Ukraniya tsawon shekaru uku da watanni ana yi. Wannan shi ne yaƙi mafi muni da samu…
Read More

Msuludu: Gwamnan Sakkwato ya ba ɗalibin da ya fita da sakamako mafi kyau a UDUS kujerar hajji

Gwamnan Jihar Sokoto, Dakta Ahmed Aliyu ya bai wa ɗalibin da ya fi kowa ƙwarewa wajen samun maki a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto (UDUS), Abdullahi Sheriff, kyautar tafiya aikin Hajji a matsayin lada kan nasarar da ya samu a karatu. An bayyana wannan kyauta ne yayin bikin yaye dalibai karo na 42 da jami’ar ta gudanar a ranar Asabar, 6 ga Satumba 2025. Abdullahi, wanda ya kammala karatunsa a fannin Microbiology da maki CGPA 4.92, ya zama dalibi mafi kwarewa a shekarar karatu ta 2023/2024. Gwamna Aliyu, wanda shima tsohon ɗalibi ne na jami’ar, ya bayyana cewa wannan kyauta na…
Read More

Hon. Abdulmumin Kofa ya karɓi kora daga NNPP bayan zargin ta da rashin adalci

Ɗan majalisa mai wakiltar Ƙiru/Bebeji a Majalisar Wakila, Hon. Abdulmumi Jibrin Kofa ya sanar da ficewarsa daga Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, inda ya ce ya amince da matakin korarsa da jam'iyyar ta yi. Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya bayyana cewa bai cancanci kora daga jam'iyyar ba, ba tare an ba shi damar kare kansa ba. Tun da farko, jam'iyyar ce ta sanar da cewa ta kore shi bisa zarginsa da karya dokokinta. Ya ce, "na yi mamakin ganin an kore ni daga NNPP. Na yi amannar cewa tattaunar…
Read More

Adadin sanatocin APC ya kai 72 yayin da na PDP da LP suka yi ƙasa a Majalisar Dattawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC na cigaba da mamaye Majalisar Dattawa yayin da adadin sanatocinta ya kai guda 72 cikin 109 bayan da Sanata Ahmed Wadada na Nasarawa ta Yamma ya koma cikinta daga SDP. Jam'iyyar PDP kuwa ta samu ragin adadi inda take da guda 28 sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye ta. Sai LP, wadda ta cigaba da riƙe guda biyar, da APGA mai biyu da kuma NNPP da SDP masu guda ɗaya kowanne. Wadada, wanda shi ne shugaban kwamitin asusun ƙasa a majalisar, ya bar APC a 2022 domin ci-gaban siyasarsa inda ya…
Read More

Hukumomin Afirka ta Kudu sun ƙi ba jirgin Super Eagles izinin sauka a ƙasar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Alamu sun bayyana cewa hukumomi a Afirka ta Kudu sun ƙi samar da wajen sauka da lokaci ga tawagar Nijeriya da suka haɗa da ƴan wasan Super Eagles da jami'ai. Hakan na zuwa ne a lokacin da tawagar ke ƙoƙarin sauka a birnin Johannesburg na ƙasar don karawa da ƴan wasan ƙasar yayin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026. Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa NFF, ta tabbatar da cewa ba a yi nasara ba yayin cimma matsaya da hukumomin ƙasar. Haka ma a yayin ji ta bakin ofishin jakadancin ƙasar. A makon…
Read More

Za a yi wa Biden aikin cutar daji ta fata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon shugaban Amurka Joe Biden, ya shiga matsalar rashin lafiyar cutar daji ta fata bayan ganin sa a wani faifan bidiyo da ke nuna shi da bandeji da tabo a goshinsa. A ranar Alhamis wani rahoto daga gidan Fox News ya ce Kakakin Biden ya tabbatar da al'amarin inda ya ce za a yi masa aikin ne domin fitar da wasu ƙananan ƙwayoyin cuta ɗaya bayan ɗaya, lamarin da ake fatan ya zama sababi warkewarsa. Da fari, Biden mai shekaru 82, ya yi jinyar cutar daji da ba a fayyace ta irinta ba a…
Read More

Kiwon lafiya: Peter Obi zai tsagaita hada-hada a bainar jama’a

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar shugaban na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sanar da tsagaita hada-hada acikin jama'a saboda matsalar kiwon lafiyarsa bayan likitansa ya shawarce shi akan haka. Obi ya bayyana haka ne ta kafar X a ranar Asabar, inda ya ce matakin ya biyo bayan ganin wasu alamu ne a sakamakon halartar taruka da yayi a ƴan kwanakin nan a jihohin Inugu, Anambra da Imo. A ranar Juma'a, Obi ya halarci taron walwalar jama'a a Inugu inda daga nan ya je asibitin Hope Specialist da ke Isulo a Ƙaramar Hukumar Orumba ta…
Read More