Za a yi wa Biden aikin cutar daji ta fata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon shugaban Amurka Joe Biden, ya shiga matsalar rashin lafiyar cutar daji ta fata bayan ganin sa a wani faifan bidiyo da ke nuna shi da bandeji da tabo a goshinsa.

A ranar Alhamis wani rahoto daga gidan Fox News ya ce Kakakin Biden ya tabbatar da al’amarin inda ya ce za a yi masa aikin ne domin fitar da wasu ƙananan ƙwayoyin cuta ɗaya bayan ɗaya, lamarin da ake fatan ya zama sababi warkewarsa.

Da fari, Biden mai shekaru 82, ya yi jinyar cutar daji da ba a fayyace ta irinta ba a bainar jama’a, wadda aka yi a matakin farko na cutar sakamakon kula da zuwa dubiya akai-akai.

Kelly Scully, wanda shi ne Kakakin nasa, ya bayyana cewa za a yi masa aikin ne da nufin taƙaice damejin fatar.

A farkon shekarar 2023 ne Biden ya fara fuskantar cutar fata inda a lokacin aka yi masa aiki a ƙirjinsa.

By Babaji