
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Alamu sun bayyana cewa hukumomi a Afirka ta Kudu sun ƙi samar da wajen sauka da lokaci ga tawagar Nijeriya da suka haɗa da ƴan wasan Super Eagles da jami’ai.
Hakan na zuwa ne a lokacin da tawagar ke ƙoƙarin sauka a birnin Johannesburg na ƙasar don karawa da ƴan wasan ƙasar yayin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa NFF, ta tabbatar da cewa ba a yi nasara ba yayin cimma matsaya da hukumomin ƙasar. Haka ma a yayin ji ta bakin ofishin jakadancin ƙasar.
A makon da ya gabata ne ofishin jakadancin ƙasar a Nijeriya ya hana biza ga wasu ƴan Nijeriya ciki har da magoya baya.
An kuma yi zargin cewa, an hana izinin sauka ga jirgin da zai yi jigilar ƴan Nijeriya zuwa ƙasar.
