Adadin sanatocin APC ya kai 72 yayin da na PDP da LP suka yi ƙasa a Majalisar Dattawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC na cigaba da mamaye Majalisar Dattawa yayin da adadin sanatocinta ya kai guda 72 cikin 109 bayan da Sanata Ahmed Wadada na Nasarawa ta Yamma ya koma cikinta daga SDP.

Jam’iyyar PDP kuwa ta samu ragin adadi inda take da guda 28 sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye ta.

Sai LP, wadda ta cigaba da riƙe guda biyar, da APGA mai biyu da kuma NNPP da SDP masu guda ɗaya kowanne.

Wadada, wanda shi ne shugaban kwamitin asusun ƙasa a majalisar, ya bar APC a 2022 domin ci-gaban siyasarsa inda ya yi nasarar lashe kujerar sanata a zaɓen 2023.

A wata takarda da ke ɗauke da kwanan wata: 2 ga Satumba zuwa ga shugaban jam’iyyar Gundumarsa ta Tudun Kofa, Wadada ya sanar da koma wa jam’iyyar mai mulki.

Lamarin da ya yi sanadin samun ƙarin mambobi ga APC a zauren majalisar zuwa 72.

By Babaji