Hon. Abdulmumin Kofa ya karɓi kora daga NNPP bayan zargin ta da rashin adalci

Spread the love

Ɗan majalisa mai wakiltar Ƙiru/Bebeji a Majalisar Wakila, Hon. Abdulmumi Jibrin Kofa ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, inda ya ce ya amince da matakin korarsa da jam’iyyar ta yi.

Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya bayyana cewa bai cancanci kora daga jam’iyyar ba, ba tare an ba shi damar kare kansa ba.

Tun da farko, jam’iyyar ce ta sanar da cewa ta kore shi bisa zarginsa da karya dokokinta.

Ya ce, “na yi mamakin ganin an kore ni daga NNPP. Na yi amannar cewa tattaunar da na yi ba su yi nauyin da za su ja min kora ba,” in shi, inda ya “ban janye komai ba a cikin abin da na fada.”

Ya ce ba a gayyace shi ba domin ya kare kansa kan abin da ake zarginsa da aikatawa, “ko a mulkin soja, ana ba wanda ake zargi dama ya kare kansa.”

Ya ce, ya so a ce ya ci gaba da zama a jam’iyyar, “Amma tunda jam’iyyar ta kore ni, dole in amince da matakin da ta dauka.”

Ɗan majalisar ya kuma ce, nan gaba kadan zai sanar da matakin da zai ɗauka a game da makomarsa a siyasa, ƙamar yadda BBCHausa ta ruwaito.

By Babaji