Msuludu: Gwamnan Sakkwato ya ba ɗalibin da ya fita da sakamako mafi kyau a UDUS kujerar hajji

Spread the love

Gwamnan Jihar Sokoto, Dakta Ahmed Aliyu ya bai wa ɗalibin da ya fi kowa ƙwarewa wajen samun maki a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto (UDUS), Abdullahi Sheriff, kyautar tafiya aikin Hajji a matsayin lada kan nasarar da ya samu a karatu.

An bayyana wannan kyauta ne yayin bikin yaye dalibai karo na 42 da jami’ar ta gudanar a ranar Asabar, 6 ga Satumba 2025. Abdullahi, wanda ya kammala karatunsa a fannin Microbiology da maki CGPA 4.92, ya zama dalibi mafi kwarewa a shekarar karatu ta 2023/2024.

Gwamna Aliyu, wanda shima tsohon ɗalibi ne na jami’ar, ya bayyana cewa wannan kyauta na nuni da muhimmancin karfafa matasa su dage wajen neman ilimi da kuma nuna godiya ga waɗanda suka yi fice.

Saidai, wannan kyauta ta jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta. Wasu na ganin kyautar ta dace da irin nasarar da Abdullahi ya samu, yayin da wasu ke ganin ya kamata a ba shi tallafi ko jari domin ci gaba da rayuwa bayan karatu, kamar yadda Jakadiya Hausa ta ruwaito.

A cewar Malam Aesha Abdullahi Shateema, “Idan ya dawo daga Hajji, me za su yi masa? Idan ba za su tallafa masa ba bayan dawowa, da ya fi a ba shi kuɗi ya fara kasuwanci.”

By Babaji