
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya yi gargaɗin cewa abin harin dakarun sojojinsa na Moscow a yanzu su ne sojojin ƙasashen Yamma da aka tura su zuwa Ukraniya.
A ranar Alhamis, ƙasashe 24 ƙarƙashin jagorancin Faransa da Birtaniya suka nemi a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bisa tsarin da Rasha ta bayar a 2022.
Dubunnan mutane yaƙi tsakanin Rasha da Ukraniya ya yi sanadin mutuwarsu yayin da ya ɗaiɗaita miliyoyi da lalata gidaje a gabas da kudancin Ukraniya tsawon shekaru uku da watanni ana yi.
Wannan shi ne yaƙi mafi muni da samu a Turai tun bayan yakin Duniya na 2.
Hukumomi a birnin Kyiv sun bayyana cewa dakarun Turai suna da muhimmanci wajen cimma yarjejeniya da Rasha, domin tabbatar da ba ta sake harba wa Ukraniya wani makami ba a nan gaba.
Kawo yanzu ƙwayen Ukraniya ba su bayyana adadin dakarun soji da suke shirin aika mata ba da adadin waɗanda za su bada gudumawarsu a yaƙin.
