PETROAN da IPMAN sun nemi Fadar Shugaban Ƙasa ta tsoma baki a rikicin Matatar Ɗangote da NUPENG

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɓangarorin raba man fetur a Nijeriya na fuskantar ƙalubale yayin da Ƙungiyar Ma’aikatan Fetur da Iskar Gas (NUPENG) ta yi barazanar tafiya yajin aiki.

NUPENG a wata sanarwa, ta bayyana cewa mambobinta za su tsunduma yajin aiki a daga ranar 8 ga watan Satumba domin nuna ƙiyayyarsu ga rashin kiyaye haƙƙoƙinsu a Matatar Ɗangote.

Tuni ƙungiyoyin ƴan kasuwar fetur da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) suka nemi gwamnatin tarayya ta tsoma baki a al’amarin.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Kamfanin Ɗangote ya shirya raba tirelolin iskar gas (CNG) guda 4,000 ga ƙananan ƴan kasuwa, lamarin da ƙungiyoyin suka ce zai yi sanadin rasa aiki ga dubunnan direbobin tirela da haifar da cikas ga tsarin gudanarwa da ake kai.

NUPENG, a wata sanarwa daga Shugaba Williams Akperha da Sakatarenta Afolabi Olawale, ta zargi Matatar da haramta wa direbobi shiga ƙungiyoyin, lamarin da ta bayyana a matsayin tauye musu ƴancin da dokokin ƙasa da na ƙasa-da-ƙasa suka tanada.

Tuni ƙungiyoyin PETROAN da IPMAN suka fara kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki mataki kan al’amarin kafin ya ta’azzara, kamar yadda suka bayyana a sanarwa mabanbanta.

By Babaji