Kiwon lafiya: Peter Obi zai tsagaita hada-hada a bainar jama’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan takarar shugaban na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sanar da tsagaita hada-hada acikin jama’a saboda matsalar kiwon lafiyarsa bayan likitansa ya shawarce shi akan haka.

Obi ya bayyana haka ne ta kafar X a ranar Asabar, inda ya ce matakin ya biyo bayan ganin wasu alamu ne a sakamakon halartar taruka da yayi a ƴan kwanakin nan a jihohin Inugu, Anambra da Imo.

A ranar Juma’a, Obi ya halarci taron walwalar jama’a a Inugu inda daga nan ya je asibitin Hope Specialist da ke Isulo a Ƙaramar Hukumar Orumba ta Kudu, wanda a kwanan nan Cocin Aguata Diocese ta saye shi.

A nan ya bada tallafin Naira miliyan 10 domin yi wa ginin asibitin kwaskwarima ta yadda za a riƙa gudanar da manyan ayyukan kiwon lafiya a cikinsa.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya bayyana cewa yayin ziyararsa ta Inugu ne ya fara jin rashin lafiya, inda ya shawarci likitocinsa, lamarin da ya sa suka nemi ya je hutun kwana ɗaya ko biyu.

By Babaji