Ranar Agaji ta Duniya: Uwargidan Gwamnan Zamfara ta tallafa wa gajiyayyu da kayan abinci

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta hannun ƙungiyar Huriyya Dauda Lawal Initiative tare da haɗin gwiwar ƙungiyar matan gwamnonin Arewa, ta gudanar da bikin ranar tallafi ta duniya, 2025 tare da tallafawa marasa galihu a Zamfara da kayan abinci don rage masu raɗaɗin talauci.

Rabi Yusuf sakatariyar hulɗa da ƴan jaridu ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Gusau.

Bikin na bana, mai taken “Speeding Global Processity don ƙarfafa tallafin al’umma,” an gudanar da shi ne a babban birnin Gusau.

Sanarwar ta bayyana cewar an tallafawa tsofaffi da marasa galihu da Kayayyakin abinci da suka haɗa da buhunan shinkafa, katan Katan na taliya, sukari, da mai na girki, da nufin samar da agajin abinci ga waɗanda suka fi buƙata.

Da take magana a madadin uwargidan Gwamnan a yayin rabon tallafin, babbar mataimakiya kan harkokin mata, Hajiya Hadiza Abubakar (Hadiza Mai H), ta bayyana cewar ƙarancin na nufin ƙarfafa dangantakar al’umma, da nuna cewa ba a manta da kowa ba.

Ta bayyana cewar ƙarancin wani nau’i ne na ganin masu ƙaramin ƙarfi musamman tsofaffi an taimake su duba da ƙalubalen matsin tattalin arziki da alumma ke ciki tare da tabbatar da tallafin ya Kai ga masu buƙata.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta sake jaddada ƙudirinta na tallafawa ƙungiyoyin mata da ƙananan yara, tana mai jaddada cewa tausayawa alummar jihar masu ƙaramin ƙarfi zai ɗore.

Waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun nuna matuƙar godiya, inda suka bayyana ƙarancin a matsayin wanda ya dace da kuma ƙara masu ƙwarin gwiwa.

“Haɗin kai tsakanin Ƙungiyar Matan Gwamnonin Arewa da Ƙungiyoyin Huriyya Dauda Lawal Initiative ya nuna irin kyakkyawar manufar da muke da ita Wajen ganin an inganta rayuwar al’umma”. Cewar Hajiya Huriyya

Uwargidan Gwamnan ta kuma yaba da sadaukarwar da ƙungiyar ta yi wajen ƙarfafa tallafin jin ƙai a tsakanin masu ƙaramin ƙarfi a faɗin yankin Arewa da ƙasa baki ɗaya.

Bikin ana gudanar dashi kowace shekara a ranar 5 ga Satumba, mai taken ranar bada agaji ta duniya.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta kuma bayyana ranar a matsayin rana mai muhimmanci da ake gudanar da ayyukan agaji a faɗin duniya wajen rage talauci, haɓaka haɗin kai, da gina al’ummomi marasa galihu.

By ukarofi