09
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Abuja, ta ce ta fara gudanar da bincike akan wata gawa da aka gano a harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, wadda aka jibge acikin mota. An gano cewa, gawar ta wani mutum ce mai suna Gaddafi Iwar ɗan shekeru 55, wanda kuma ɗan ƙabilar Tibi ne. Haka kuma, lebura ne shi a wani wajen aikin gini da ke kewayen majalisar.. An gano gawar ne a wata mota ƙirar 'Peugeot 406' mai lambar BWR-577 BF da misalin ƙarfe 9 na daren Lahadi wayewar Litinin. Lamarin da ya jefa ma'aikata da masu…
