10
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe INEC, ta tabbatar da jagorancin jam'iyyar adawa ta ADC a ƙarƙashin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Bonaventure Mark, lamarin da ya kawo ƙarshen taƙaddamar shugabanci a tsakanin ƴaƴanta tsawon watanni. A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, INEC ta zayyano sunayen mambobin kwamitin ayyukan (NWC) jam'iyyar, wanda hakan ke nufin ƴan ɓangaren David Mark su ne sahihan jagororin ADC. Ga yadda INEC ta jero su: Sanata David Mark – Shugaban jam'iyya na Ƙasa, Ogbeni Rauf Aregbesola (tsohon gwamnan Jihar Osun) – Sakatare; Dakta Mani Ibrahim Ahmad –…
