
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe INEC, ta tabbatar da jagorancin jam’iyyar adawa ta ADC a ƙarƙashin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Bonaventure Mark, lamarin da ya kawo ƙarshen taƙaddamar shugabanci a tsakanin ƴaƴanta tsawon watanni.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, INEC ta zayyano sunayen mambobin kwamitin ayyukan (NWC) jam’iyyar, wanda hakan ke nufin ƴan ɓangaren David Mark su ne sahihan jagororin ADC.
Ga yadda INEC ta jero su: Sanata David Mark – Shugaban jam’iyya na Ƙasa, Ogbeni Rauf Aregbesola (tsohon gwamnan Jihar Osun) – Sakatare; Dakta Mani Ibrahim Ahmad – Ma’aji; Akibu Dalhatu – Sakataren Kudi; sai Farfesa Oserheimen Aigberaodion Osunbor (tsohon gwamnan Edo) – Mai bada shawara akan harkar shari’a
Tabbatarwar da INEC ta yi wa jagororin ɓangaren ya nuna kawo ƙarshen rikicin cikin gida da jam’iyyar ta riƙa fuskanta a ƴan shekarun nan.
Haka kuma, masu sharhi akan al’amuran siyasa suna ganin samun jagoranci irin na ƴan siyasa kamar su David Mark da Aregbesola abu ne da ka iya ƙarfafa matsayin jam’iyyar acikin sauran jam’iyyun siyasar Nijeriya da kuma zama babban ƙalubale a zaɓen 2027.
Tuni masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka yi maraba da ci-gaban, lamarin da zai taimaka wajen samar da ɗorewa, haɗin kai da dabarun gudanarwa acikinta kamar yadda suka bayyana.
A cewarsu, abinda ya rage wa ADC a yanzu shine ƙoƙarin neman goyon baya ɗaga tushe da haɗa kan mambobinta a sassan ƙasar, gami da ƙulla ƙawance a inda ya dace domin gogayya da jam’iyya mai mulki ta APC da babbar ta adawa, wato PDP.
