NSCDC a Katsina ta daƙile ƙoƙarin karkatar da gidan sauro a Matazu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Maganin sauron da ke haɗe da maganin zazzaɓin cizon sauro, hukumar kula da kiyon lafiya a matakin farko ta samar kyauta domin rabawa al’ummar jihar.

A zirga zirga da take yi na tabbatar da tsaro jami’an tsaron na farin kaya suka ci tare haya buɗaɗɗa ɗauke da buhu 35 na gidan sauro.

Kowane buhu yana ɗauke da gidan sauro 50 da motar ta ɗauko daga garin Matazu akan hanyar ta na zuwa Kano.

Nan take suka kama direban motar zuwa hedkwatar hukumar a Katsina.

A yayin gudanar da bincike kamar yadda hukumar ta sanar direban ya ce wasu mutane suka ɗauke shi haya a kasuwar Charanchi ya ɗaukar masu kaya daga garin Matazu zuwa Kano.

Direban ya ƙara da cewa shi bai san me ke cikin buhun an da ya ɗauka a motar sa ba.

Tuni dai mutane huɗu da ake zargi da mallakan gidan sauron suka ranta ana kare.

Kwamandan hukumar Aminu Datti Ahmad ya ce hukumar ba za tai ƙasa a gwiwa ba wajen kama mutanen da ake zargi da neman karkatar da gidan sauron domin fuskantar Shari’a.

Ya bayyana ƙudirin hukumar na cigaba da yaƙi da masu lalata kayan gwamnati,masu yiwa tattalin arziki zangon ƙasa da sauran ɓata gari a jihar Katsina.

Kwamandan ya yabawa al’ummar jihar bisa goyon baya da suke baiwa hukumar,sai yayi kira ga mutane da taimaka wajen bada bayanai na sirri da zai gano maɓoyan bata gari a faɗin jihar.

By ukarofi