Rumbun lantarki na ƙasa ya sake lalacewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Laraba al’ummar Nijeriya suka sake shiga halin rashin wutar lantarki a yayin da rumbun lantarki na ƙasar ya sake lalacewa a wani karo.

Al’amarin ya auku ne a tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na rana, lamarin da ya jefa miliyoyin jidaje da kasuwanci acikin duhu.

Tuni kamfanonin raba wutar lantarki a sassan ƙasar, wato DisCos suka tabbatar da al’amarin, inda suka ce hakan ya faru ne a sakamakon lalacewar wani rukunin gudanarwa a babban kamfanin lantarki na ƙasa TCN, wanda ke gudanar da rumbun na ƙasa.

A wani saƙo da na Abuja (AEDC) ya wallafa ta kafar X, ya ce al’amarin ya faru ne a sakamakon rashin samun wuta daga rumbun na ƙasa tun da misalin ƙarfe 11:23 na safe, wanda ya shafi ɓangarorin da yake raba wa lantarki.

Haka ma na Fatakwal (PHED), wanda ya sanar da lalacewar a wani saƙo, inda ya ce dukkan jihohin da yake ba wuta, al’amarin ya shafe su, wato Ribas, Bayelsa, Akwa-Ibom da Kuros-Riba.

AEDC da PHED sun kuma bai wa kwastomomi haƙuri kasancewar tuni injiniyoyi suka fara aikin shawo kan matsalar.

By Babaji