
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma a Ƙaramar Hukumar Yagba da ke Jihar Kogi sun shiga damuwa a ranar Laraba yayin da wasu mahara ɗauke da muggan makamai suka far wa jami’an ƴan sanda hari a wani rukunin bincike, inda suka halaka jami’ai uku da tserewa da bindigunsu.
Lamarin ya auki ne a wajen bincike na yankin Ofili akan hanyar Egbe zuwa Okunran zuwa hanyar Pategi, inda mutane da dama suka shiga fargaba bisa ƙamarin taɓarɓarewar tsaro a yankunan masarautar Okun da ƙara kiraye-kirayen ɗaukar matakin gaggawa a kai.
Shaidu sun tabbatar da cewa, al’amarin ya faru ne a lokacin da jami’an suke ƙoƙarin isa wajen aikinsu, inda maharan suka buɗe wa motarsu ƙirar Hilux wuta. Tuni jami’ai biyu suka rasu a nan take kana daga bisani na ukun ya bi su a Asibitin E-Unit ECWA.
Da yake tabbatar da al’amarin, Shugaban ƙaramar hukumar, Tosin Olokun ya bayyana jami’an da suka rasa rayukan nasu a matsayin jarumai da suka sadaukar da rayukansu a bakin aiki.
A sanarwar da Sakataren yaɗa labaransa, Adeyemi Babarinde ya fitar a ranar Lahadi, Olokun ya koka game da faruwar al’amarin tare da jajenta wa rundunar ƴan sanda da iyalan waɗanda suka rasu da kuma ɗaukacin al’ummar gari.
Ana ganin hakan a matsayin abinda ke nuna tabbacin yaɗuwar ƙungiyoyin ƴan ta’adda da ke ayyukansu a ƙauyukan jihar da ma jihohin maƙota.
