11
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Majalisar Dokoki ta Jihar Benuwai ta rushe tawagar jagororinta, inda ta bar kaɗai Kakakinta, Alfred Emberga da Mataimakinsa, Lamin Danladi. An ɗauki matakin ne yayin zaman majalisar na ranar bayan miƙa ƙudirin hakan daga tsohon mataimakin jagoran mafi rinjaye na majalisar, wato Douglas Akya. Akya ya ce, tunda ƙaramar hukumarsu ɗaya da na Kakakin, kuskure ne a ce ya cigaba da zama a matsayin mataimakin jagoran mafi rinjaye. Bayan miƙa ƙudirin ga fagen zaɓe, mambobin majalisar suka amince da shi. Daga nan aka naɗa muƙaman ga Pharm. Thomas Dugeri (APC/Kwande West)…
