12
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta samu wani saƙo na musamman daga Amurka ko Ghana ba akan rahotannin da ke cewa akwai ƴan Nijeriya daga cikin waɗanda Amurka ta koro zuwa Ghana daga birnin Washington. Haka na zuwa ne a lokacin da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa daga cikin mutane 14 da Amurka ta koro akwai ƴan Nijeriya da ƴan wasu ƙasashen yammacin Afirka a ƙarƙashin shirin karɓarsu a ƙasar kafin kai su ƙasashensu. Akan haka ne Kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa ya shaida wa jaridar News Point…
